Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan ƙungiyoyi na gogayya kan Musiala, Utd da Arsenal sun haƙura da Rabiot
Liverpool ta ƙara tashi tsaye wajen bayyana sha'awarta a kan ɗan wasan tsakiya na Bayern Munich Jamal Musiala, na Jamus mai shekara 21, wanda Manchester City da Real Madrid da Paris St-Germain duka suke sa ido a kanshi. (Caughtoffside)
Manchester United ta samu ƙwarin gwiwa a zawarcin ɗan wasan gaba na gefe na Paris St-Germain Xavi Simons, kasancewar matashin ɗan wasan na tawagar Holland, mai shekara 21, da yake zaman aro yanzu a RB Leipzig, ba ya sha'awar ci gaba da zama a PSG. (Teamtalk)
Manchester United da Arsenal sun haƙura da zawarcin ɗan wasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 29, wanda ba shi da ƙungiya a yanzu, saboda albashin da yake buƙata na fan 220,000 a duk mako. (GiveMeSport)
Manchester United ta sanya sunan ɗan wasan gaba na Lille Jonathan David, na Kanada mai shekara 24, da kuma, Ivan Toney, ɗan Ingila, mai shekara 28 da ke Al-Ahli a matsayin waɗanda za ta saya idan ba ta samu damar sayen Joshua Zirkzee, na Holland ba, mai shekara 23, daga Bologna. (ESPN)
Inter Milan na sha'awar sayen ɗan wasan tsakiya na Aston Villa Jacob Ramsey, ɗan Ingila mai shekara 23. (Caughtoffside)
Ɗan wasan gaba na Chelsea da Ivory Coast David Datro Fofana ya amince ya tafi ƙungiyar Goztepe SK ta Turkiyya, aro, bayan da maganar tafiyarsa AEK Athens ta ruguje. (Fabrizio Romano)
West Ham na sha'awar ɗaukan tsohon ɗan bayan Liverpool Joel Matip, mai shekara 33, wanda har yanzu ɗan bayan na Kamaru haifaffen Jamus ba shi da ƙungiya. (Ruhr24 - in German)
Tsohon ɗan bayan Ingila da Chelsea Ashley Cole zai bar aikinsa na kociya a Birmingham City, domin kama aiki da hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila da taimaka wa kocin riƙon-ƙwarya na Ingila Lee Carsley. (Athletic )
Ɗan bayan Chelsea Ben Chilwell ɗan Ingila, yana fatan a sanya shi cikin ƴan wasa 25 na ƙungiyar da ke mata wasa a gasar Premier, saboda ba ya son tafiya aro Turkiyya. (Telegraph)
Arsenal da Chelsea za su ci gaba da barin ɗan gaban Sporting Lisbon Viktor Gyokeres, na Sweden mai shekara 26, cikin jerin ƴan wasan da suke son saye a bazara mai zuwa. (Football Insider)
Junior Firpo na son ƙulla sabon kwantiragi a Leeds amma kuma ɗan bayan na Jamhuriyar Dominican na da damar komawa gasar La Liga idan ba su cimma matsaya ba, kuma Real Betis na matuƙar soshi. (Teamtalk)
Tsohon ɗan bayan Real Madrid Sergio Ramos, mai shekara 38, na duba yuwuwar tafiya gasar Amurka, ta Major League Socce, bayan da yunƙurin ɗan wasan na Sifaniya na tafiya Botafogo ta Brazil ya ci tura. (Goal)
Wakilin ɗan wasan gaba na gefe na Athletic Bilbao Nico Williams, ya ce ɗan Sifaniyan mai shekara 22, ya yi watsi da maganar tafiyarsa Barcelona, saboda yana son ci gaba da zama a ƙungiyarsa tsawon ƙarin shekara ɗaya. (AS)
Masu AC Milan ba sa jin daɗi na halayyar tsohon ɗan gaban Sweden Zlatan Ibrahimovic mai shekara 42, a aikin da yake musu na babban mai bayar da shawara ga ƙungiyar. (La Repubblica)