Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugaban Marseille bai yi nadama kan ɗaukar Greenwood ba
Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Olympique Marseille Pablo Longoria ya ce kulob ɗin ya yi nazari kan duk bayanan da suka dace lokacin da ya sayi Mason Greenwood daga Manchester United kuma bai yi nadama kan yarjejeniyar ba.
Greenwood, mai shekara 22, ya bar Old Trafford a kan fam miliyan 26.6 zuwa kulob ɗin na Faransa a watan Agusta, inda ya sanya hannu har zuwa 2029.
A watan fabrairun 2023 ne dai aka yi watsi da manyan tuhume-tuhumen da ake yi wa Greenwood da suka jiɓanci yunƙurin fyaɗe da kai kuma cin zarafi.
Sai dai Marseille ta fuskanci suka daga magajin garin wanda ya bayyana matakin a matsayin 'abin da bai dace ba' a lokacin da ƙungiyar ke son siyan ɗan wasan gaban wanda ya shafe kakar wasa guda a matsayin aro a Getafe da ke ƙasar Sifaniya.
Greenwood ya ci ƙwallo biyar a wasanni uku tun bayan komawarsa ƙungiyar ta Ligue 1.
Ƙwallayen da Greewood ya ci sun taimaka wa Marseille ta fara kakar bana da ƙafar dama inda ba ta yi rashin nasara ba ya zuwa yanzu duk da cewa dai an yi wa kulob ɗin garambawul tun zuwan sabon koci Roberto De Zerbi daga Brighton a bazarar da ta gabata.