Ten Hag ya yi watsi da sukar da Ronaldo ya yi masa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Manchester United Erik Ten Hag ya yi watsi da sukar da Cristiano Ronaldo ya yi na baya-bayan nan kuma ya ce hayaniyar da ake yi kan kulob ɗin ba ta dame shi ba.

A wata hira da ya yi da tsohon abokin wasansa na United Rio Ferdinand, Ronaldo ya ce Ten Hag ya yi kuskuren cewa ƙungiyar na da sauran aiki a gabanta kafin ta iya lashe gasar Premier League a karon farko tun shekarar 2013.

Ko da yake Ronaldo ya ci gaba da cewa shi ma yana tunanin tsohuwar ƙungiyar tasa ba za ta iya lashe gasar ba, yana jin a matsayinsa na mai horaswa Ten Hag bai kamata ya yi irin wannan furucin ba.

Da aka tambaye shi game da kalaman tsohon ɗan wasan gabanin tafiyar da United za ta yi zuwa Southampton a ranar Asabar, Ten Hag ya ce Ronaldo ya sake nanata abin da shi ma ya faɗa ne.

"Yana da ƴancin bayyana ra'ayinsa, ba laifi ba ne, yana can a Saudiyya, nesa da Manchester." in ji shi

Bayan rashin nasara a jere a wasanninta da Brighton da kuma Liverpool, United ta nufi Southampton da sanin cewa idan ta yi rashin nasara wanan zai zame farkon kakar wasa mafi muni da ta yi tun kakar 1986-87, lokacin da aka kori Ron Atkinson aka maye gurbinsa da Sir Alex Ferguson.

Yawancin masu bibiyar harkokin ƙwallon ƙafa sun yi imanin cewa kocin mai shekaru 54 ba zai tsira da aikinsa har ƙarshen kakar bana ba sakamakon ƙarin madafan iko da Sir Jim Ratcliffe ya samu a kulob ɗin.