Man Utd za ta nemi Tuchel bayan Inzaghi ya ƙi, Madrid na harin Duran

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta nemi sake tattaunawa da tsohon kociyan Chelsea Thomas Tuchel idan ta kori Ten Hag. (ipaper)
Manyan shugabannin United za su gana ranar Talata domin tattauna batun halin da ƙungiyar ke ciki bayan ɗaya daga cikin waɗanda suka mallake ta, Sir Jim Ratcliffe ya kalli wasanta da Aston Villa na gasar Premier ranar Lahadi. (Athletic)
Shi kuwa kociyan Inter Milan Simone Inzaghi ya yi watsi da tayin da aka yi masa na aikin kociyan United ɗin, inda zai gaji Ten Hag (Sportitalia)
Tsohon mai horad da ƴan wasan Manchester United Rene Meulensteen ya ce a shirye yake ya koma aikin idan Ruud van Nistelrooy, wanda a yanzu yake mataimakin kociya a ƙungiyar zai samu aikin. (No Tippy Tappy Football Podcast, daga Mirror)
Real Madrid na sa ido sosai a kan matashin ɗan wasan gaba mai kai hari na Aston Villa Jhon Duran, na Kolombiya mai shekara 20. (Football Insider)
Arsenal na son matashin ɗan wasan gaba na Barcelona, Arnau Pradas, mai shekara 18, na tawagar ƴan ƙasa da shekara 19 ta Sifaniya. (Mundo Deportivo)
Manchester City ta tattauna a kan ɗan wasan tsakiya na Crystal Palace Adam Wharton,ɗan Ingila mai shekara 20, a matsayin wanda zai maye gurbin Rodri da ya ji rauni. (Football Insider)
Everton za ta yi ƙoƙarin dawo da tattaunawa a kan sabon kwantiragi da ɗan wasan Ingila mai kai hari Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 27, idan maganar sayen ƙungiyar da Friedkin Group za su yi ta tabbata. (ipaper)
Liverpool na matuƙar son sayen ɗan gaban Ingila Eberechi Eze, mai shekara 26, daga Crystal Palace. (Football Insider)
Barcelona da Atletico Madrid na son sayen ɗan wasan tsakiya na Arsenal Thomas Partey, na Ghana mai shekara 31. (Fichajes, daga TeamTalk)










