An haramta wa ɗanwasan da ya yi cizo wasa takwas a Ingila

Milutin Osmajic bites Blackburn's Owen Beck

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon Ingila ta haramta wa Milutin Osmajic ɗanwasan Preston North End buga wasa takwas saboda cizon Owen Beck ɗanwasan Blackburn.

Ɗanwasan mai shekara 25 na Montenegro, wanda ya amince da laifin an ci tararsa fam dubu 15.

Osmajic ba zai buga wa ƙungiyarsa wasa ba har sai wasanta da Derby a ranar 23 ga Nuwamba.

Hukumar FA ta ce za ta wallafa dalilin ɗaukar matakin, yayin da ƙungiyar Preston ta ce ba za ta ƙara cewa komi ba har zuwa lokacin.

Kafin haramcin ga Osmajic, daraktan Preston Peter Ridsdale ya shaida Talksport cewa ɗanwasan na gaba ya amince da tuhumar kuma zai fuskanci mataki na ladabtarwa.

Osmajic, wanda dawo ƙungiyar daga Cadiz a Satumban 2023, ya ci ƙwallaye 11 a wannan kakar ciki har da biyu da zura a ranar Watford a ranar Laraba.

An taɓa haramta wa Luis Suarez, tsohon ɗanwasan Liverpool, buga wasa 10 bayan cizon ɗanwasan Chelsea Branislav Ivanovic.