Hotunan yadda ake yin buɗe-baki a Gaza

المسحراتي يسير في شوارع خام يونس المدمرة لإيقاظ الفلسطينيين لتناول وجبة السحور الأولى في شهر رمضان المبارك، فجر 1 مارس/آذار 2025

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu tashe sun rika bi layi-layi ta cikin ɓaraguzan gini a Khan Younis domin tayar da mutane yin sahur a ranar 1 ga watan Maris, 2025
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Duk da yaƙin da aka gwabza wanda ya ɗaiɗaita Zirin Gaza, mutanen yankin sun samu ƙwarya-ƙwaryar farin ciki.

Yayin da a lokacin azumin Ramadan na bara al'ummar yankin ke cikin matsatsi sanadiyyar ruwan bama-bamai daga sojojin Isra'ila, a wannan karon abin ya zo da bambanci.

A wannan karo iyalai da dama sun samu damar haɗuwa domin yin buɗe-baki a tare, wani abu da ba su samu damar yi ba tun shekarar 2023.

BBC ta tattauna da wasu ƴan Gaza, jim kaɗan bayan shan ruwa a azumin da suka kai na farko.

بائع يقدم التمور للزبائن في متجر بسوق الزاوية القديم في مدينة غزة في اليوم الأول من شهر رمضان المبارك في الأول من مارس 2025

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata kasuwa da ake kira tsohuwar kasuwar Zawiya Market da ke birnin Gaza a ranar farko ta azumin Ramadan

Ahmed Karim, da ke zaune a unguwar Al-Tuffah a birnin Gaza, arewacin Zirin Gaza ya bayyana farin ciki kan zuwan Ramadan na wannan shekara, ya ce babu abi da yake tunawa a baya sai "yaƙi da ruwan bama-bamai."

Karim ya ce ya samu damar yin buɗe-baki tare da ƴan'uwa, wani abu da bai samu ba a bara, inda ya ce "kowa ya tarwatse, kuma babu abinci a bara, yanzu kuwa akwai."

أسرة غزاوية تجلس على طاولة طعام في أحد شوارع غزة استعدادا لتناول طعام الإفطار في أول يوم في رمضان

Asalin hoton, Reuters

Babu yabo ba fallasa

Ita kuwa Umm Abed Al-Ghafri ta bayya cewa har yanzu hankalinta ba a kwance yake ba kasancewar ana cikin yanayi na fargaba duk kuwa da sauƙin da aka samu a bana da kuma abinci da aka samu, inda a bara babu.

بائع يرش التوابل على طبق من الحمص من كشكه في سوق الزاوية القديم بمدينة غزة في اليوم الأول من شهر رمضان المبارك في الأول من مارس 2025

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Old Zawiya Market in Gaza City on the first day of Ramadan 2025

Ghassan Hamdan da ke zaune a Beit Hanounya ce duk da cewa wannan azumin ya fi na bara, amma bai yi daidai da yadda ake yin azumin ba kafin ɓarkewar yaƙi, ksancewar yanzu shi da matarsa da yara ne kawai suke tare, sauran iyalin da kuma abokai kuma na wani wuri na daban.

"Muna rayuwa ne yanzu nesa da gida, wanda aka ruguza a lokacin yaƙi, inda yanzu muka yi nisa da iyalanmu.

Yanzu muna rayuwa ne cikin mutanen da ba mu san su ba su ma ba su san mu ba."

فلسطينيون يتناولون الطعام أمام طاولة ممتدة في شوارع غزة

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Falasɗinawa na cin abinci kan wuraren da aka tanada a gefen tituna

"Muna kewar azumin shekarun baya"

غزيون يؤدون صلاة التراويح في أول أيام شهر رمضان

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yadda mazauna Gaza suka yi sallar asham a ranar farko ta azumin Ramadan

Duk da cewa akwai yarjejeniyar tsagaita wuta da ke aiki, amma akwai iyalai da dama waɗanda ba su samu damar haɗuwa da ƴan'uwa domin yin buɗe-baki ba a wannan wata na Ramadan.

Youssef Al-Tawil ya kwatanta azumin wannan shekara da kuma na lokacin zaman lafiya, lokacin da yakan zuwa tare da iyayensa biyu da sauran yara domin yin buɗe baki.

فلسطينيون يفطرون بتناول وجبات الإفطار خلال شهر رمضان المبارك، بالقرب من أنقاض المباني، وسط وقف إطلاق النار بين إسرائيل وحماس، في رفح، جنوب قطاع غزة

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yadda aka yi buɗe-baki a ranar farko na azumin Ramadan a Rafah da ke kudancin Gaza

Al-Tawil ya shaida wa BBC cewa yana rayuwa ce ta baƙin ciki dun kuwa da zuwan Ramadan, sanadiyyar tarwatsewar iyalinsa.

"Ina cikin wani tanti, ɗan'uwana ma na a wani tantin a wani wurin na daban, wuri mai nisa da juna," ya yi bayanin cewa suna "yin ƙarfin hali ne kawai wajen ci gaba da rayuwa, amma suna kewar lokutan azumi na baya."

فتى فلسطيني يشعل الألعاب النارية بالقرب من أنقاض مبنى خلال احتفاله باليوم الأول من شهر رمضان في مخيم البريج للاجئين في وسط قطاع غزة في الأول من مارس 2025

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasan tartsatsin wuta a kan wani rusasshen gini a sansanin ƴan gudun hijira na Bureji a yankin tsakiyar Gaza

Yayin da Abu Hisham ke bayyana damuwa da takaici, ya ce watan Ramadan a wannan shekara ya zo "lami bayan an tarwatsa mu, rayuwa a cikin tanti babu daɗi".

نساء يعدن الطعام للإفطار في اليوم الأول من شهر رمضان المبارك، بينما يجلسن بجوار أنقاض مبنى منهار في ملجأ في جباليا شمال قطاع غزة في الأول من مارس/آذار 2025

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda ake shirya kayan buɗe-baki a ranar farko ta watan Ramadan a wani rusasshen gini da ke Jabalia

Abu Hashem ya ce a baya mutanen Gaza na buɗe-baki ne da markaɗaɗɗiyar kaza a ranar farko ta Ramadan, kuma ya ce yakan tayar da mutane su yi sahur da asuba.

"Yanzu duk babu irin wannan, kuma ko mutum ya yi niyyar yin hakan za ka ji kamar ba da gaske ba ne."