United ba ta cire rai kan Champions League ba - Ten Hag

Ten Hag

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kocin Manchester United Erik Ten Hag ya ki yin ƙasa a gwiwa wajen samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai na kaka mai zuwa duk da cewa a yanzu akwai tazarar maki 11 tsakanin ƙungiyarsa da Aston Villa wadda ke matsayi na huɗu a kan teburi.

Sabon mai hannun jari Sir Jim Ratcliffe ya sanya fifiko kan shiga gasar kakar wasa ta gaba.

Amma rashin nasarar da United ta yi a Manchester City da ci 3-1, na nufin a yanzu suna buƙatar Villa ta yi gagarumin tuntuɓe, ko kuma gasar Premier ta samu ƙarin gurbi a sabon tsarin gasar ta zakarun Turai.

Duk da haka, United za ta buƙaci Tottenham da ke matsayi na biyar ta fuskanci babban ƙalubale domin a halin yanzu maki 6 ne ke tsakanin ƙungiyoyin biyu, kuma Tottenham na da kwanten wasa ɗaya.

United na da jan aiki a gabanta ganin cewa ta riga ta yi wasa da Villa da Tottenham sau biyu, ko da yake ƙungiyoyin biyu za su kara da juna a Villa Park ranar Lahadi mai zuwa.

Ingila za ta samu gurbi biyar na gasar cin kofin zakarun Turai idan ƙungiyoyin Premier suka yi ƙwazo a dukkanin gasannin Turai uku a wannan kakar.