Barcelona ta sayi Raphinha daga Leeds United kan £55m

An wallafa

Barcelona ta sayi dan wasan gaba na Brazil Raphinha daga Leeds United a kan farashin da ya kai £55m.

An gabatar da dan wasan, mai shekara 25, ga magoya bayan kungiya a filin wasan Catalan ranar Juma'a.

Raphinha, wanda ya koma Leeds daga kungiyar kasar Faransa Rennes a kan £17m a 2020, ya murza leda sau 65 a Gasar Firimiya a kungiyar ta Yorkshire club, inda ya ci kwallo 17 sannan ya taimaka aka ci 12.

"Tun ina karamin yaro nake burin zuwa wannan kungiyar," a cewar Raphinha a hirarsa da Barca TV.

"Zan yi bakin kokarina."

Leeds United ta yaba wa Raphinha a sanarwar da kungiyar ta fitar yayin da take tabbatar da rabuwa da dan wasan: "Muna son tarihi ya sani cewa muna mika godiyarmu ta musamman ga Raphinha saboda da gudunmawar da ya bai wa kungiyar ta kwallon kafa.

"Ya zage dantse sosai har zuwa lokacin da ya kammala zamansa a Elland Road kuma gudunmawarsa a filin wasa na Brentford ba za ta gushe daga tunaninmu ba."

Raphinha ya ci fenaretin da Leeds ta yi nasara da ci 2-1 a karawarsu da Brentford a ranar karshe a kakar wasa ta 2021/22 lamarin da ya sa suka samu gurbi a Premier League.