Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ta kara kwantiragin kaka biyu ga Dembele
Barcelona ta kara kwantiragin kaka biyu ga dan kwallon tawagar Faransa, Ousmane Dembele, domin ya ci gaba da taka leda a Camp Nou.
A karshen kakar tamaula da ta wuce yarjejeniyar dan kwallon mai shekara 25 ya kare a kungiyar, yanzu an tsawaitata zuwa karshen 30 ga watan Yunin 2024.
Dembele ya koma Barcelona daga Borussia Dortmund a 2017 kan kwantiragin fam miliyan 96.8 da karin tsarabe - tsarabe da ta kai fam miliyan 135.5.
Ya ci kwallo 32 ya bayar da 34 aka zura a raga a wasa 150 da ya yi wa Barca.
Dan wasan ya yi fama da jinya karo da yawa, sai dai ya bayar da kwallo 13 aka zura a raga, shi kuma ya ci biyu a wasa 32 a kakar da ta wuce.
An yi ta alakanta Dembele da cewar zai koma taka leda a kungiyoyin Premier League da yawa, ciki har da Chelsea da kungiyar Faransa, Paris St-Germain.