Chelsea na son Alonso, Inter Miami za ta yi wa Messi tayin hannun jari

Xhabi Alonso

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alonso ya taka leda a Liverpool da Real Madrid da Bayern Munich
An wallafa

A shirye Inter Miami take ta bai wa Lionel Messi hannun jari a kungiyar ta gasar Amurka domin shawo kansa ya koma can da taka leda a bazara. (Independent)

Leicester za ta nemi kusan fam miliyan 50 daga duk kungiyar da ke sha'awar dan wasanta na tsakiya James Maddison, dan Ingila, kuma ana ganin Tottenham ce ke kan gaba wajen zawarcin matashin mai shekara 26. (Telegraph)

Kociyan Bayer Leverkusen Xabi Alonso ya samu shiga cikin wadanda Chelsea za ta zaba domin maye gurbin Graham Potter. (Guardian)

Arsenal ta fara tattaunawa da dan wasan tsakiya na Leicester City Youri Tielemans dan Belgium.

Amma kuma Newcastle United da Barcelona ma na sha'awar dan wasan mai shekara 25. (Football Insider)

Chelsea ta fara tattaunawa da dan wasanta na tsakiya N'Golo Kante, a kan sabon kwantiragi. (Fabrizio Romano)

Leicester City na duba yuwuwar daukar wani kwararren kociyan rikon-kwarya kamar Martin O'Neill ko Rafa Benitez, domin maye gurbin Brendan Rodgers har zuwa karshen kaka. (Independent)

Kungiyar tana nazari a kan Graham Potter, wanda Chelsea, ta kora kwanan nan, da kociyan Brentford Thomas Frank. Shi ma tsohon kociyan Southampton Ralph Hasenhuttl da tsohon kociyan Leeds Jesse Marsch, na cikin wadanda Leicester din ke nazari a kansu. (Sky Sports)

Haka shi ma tsohon mai horad da Borussia Monchengladbach Adi Hutter zai iya samun aikin Leicester din. (Mail)

Haka kuma Leicester din ta kasance a gaba-gaba cikin kungiyoyin da ke zawarcin mai tsaron ragar Valencia Giorgi Mamardashvili dan kasar Georgia. (Fabrizio Romano)

Burnley na son sayen matashin dan wasan gaba na gefe na Ajax, Sontje Hansen, dan kasar Holland mai shekara 20 a bazaran nan. (Football Insider)

Arsenal na tattaunawa da wakilan Reiss Nelson a kan tsawaita kwantiragin dan wasan gaban dan Ingila. (Fabrizio Romano)