Man United ta kasa daukar fansa a kan Bournemouth

Bournemouth da Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar Asabar Manchester United ta je ta tashi 2-2 a gidan Bournemouth a wasan mako na 33 a Premier League.

A minti na 16 da fara wasa ne Bournemouth ta fara cin kwallo ta hannun Dominic Solanke daga baya Bruno Fernandes ya farke saura minti 14 su je hutu.

Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne Bournemouth ta kara na biyu ta hannun Justin Kluivert, sai Fernandes ya kara farkewa a bugun fenariti.

Da wannan sakamakon Manchester United ta koma ta bakwai da maki 50 ranar Asabar, ita kuwa Bournemouth mai maki 42 tana ta 12.

Ranar 9 ga watan Disamba, Bournemouth ta je Old Trafford ta doke United 3-0, inda Dominic Solanke da Philip Billing da kuma Marcos Senesi suka ci mata kwallaye.

Manchester United wadda ta kare ta ukun teburin Premier a bara na fatan daukar koda kofi daya ne a bana, wadda take cikin FA Cup zagayen daf da karshe.

Ranar 21 ga watan Afirilu United za ta buga zagayen daf da karshe da Coventry City a FA Cup a Wembley.

Tuni aka yi waje da United a cikin rukuni a Champions League a bana, sannan Newcastle United ta fitar da ita a Carabao Cup, wanda ta lashe a bara.

Wasannin dake gaban Manchester United a bana:

FA Cup Lahadi 21 ga watan Afirilu

  • Coventry da Man United

Premier League Laraba 24 ga watan Afirilu

  • Man United da Sheff United

Premier League Asabar 27ga watan Afirilu

  • Man United da Burnley

Premier League Litinin 6 ga watan Mayu

  • Crystal Palace da Man United

Premier League Lahadi 12 ga watan Mayu

  • Man United da Arsenal

Premier League Laraba 15 ga watan Mayu

  • Man United da Newcastle

Premier League Lahadi 19 ga watan Mayu

  • Brighton da Man United