Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal za ta yi wasa biyar cikin watan Satumba
Arsenal ta fara kakar bana da kafar dama, wadda ta hada maki 12 a wasa hudu a kakar Premier League ta 2022/23.
Cikin wasannin da ta yi ta ci kwallo 11 an zura mata biyu a raga da karawa biyu ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba.
Ranar 5 ga watan Agusta ta fara da cin Crystal Palace 2-0 a Selhurst Park, kuma Gabriel Martinelli ne ya ci mata kwallo sai Marc Guehi na Palace da ya ci gida.
Arsenal ta fara wasa a gida ranar 13 ga watan Agusta, inda ta doke Leicester City 4-2 a Emirates, Gabriel Jesus ne ya zura biyu sai Granit Xhaka da Gabriel Martinelli da kowannensu ya ci daya.
Wasa na uku kuwa Gunners zuwa ta yi ta casa Bournemouth 3-0 ranar 20 ga watan Agusta, kyaftin Martin Odegaard ne ya zura biyu a raga da kuma William Saliba.
Arsenal ta ci wasa na hudu a jere ranar 27 ga watan Agusta, inda ta doke Fulham 2-1 a wasan hamayya a Emirates, Martin Odegaard da Gabriel suka samar mata maki ukun da take bukata.
Arsenal ta yi wannan gwanintar bayan da ta dauko sabbin 'yan wasa a bana ciki har da Gabriel Jesus da Zinchenko.
Gunners ta nuna cewar a shirye take ta yi gogayya da kungiyoyi kamar Liverpool da Chelsea da Tottenham da Manchester City wajen lashe Premier League a bana.
Tottenham tana cikin wadanda za a yi gwa-gwa-gwa da ita, Manchester United ma na son yin abin a zo a gani, shi ya sa take ta yin cefane.
Ranar 31 ga watan Agusta Arsenal za ta karbi bakuncin Aston Villa a wasan mako na biyar a gasar Premier League.
Aston Villa ba ta kokari sosai a kakar nan, wadda ta ci wasa daya, tana ta 15 a kasan teburi mai maki uku a wasa hudun da ta kara.
Daga nan Gunners za ta fuskanci karawa biyar a cikin watan Satumba, ciki har da fafatawa biyu a Europa League.
Wasa biyar da Arsenal za ta yi cikin watan Satumba
Arsenal za ta ziyarci Old Trafford domin fuskantar Manchester United a wasan farko cikin watan Satumba.
Daga nan Arsenal za ta je Zurich, domin buga wasan farko a cikin rukuni da za ta kara a Europa League, bayan da ta yi ta biyar a kakar da ta wuce a teburin Premier League.
Arsenal za ta buga wasan Premier na gaba da Everton a Emirates fafatawa ta uku a cikin watan na Satumba.
Gunners za ta kara wasa na biyu a gida amma a Europa League da PSV Eindhoven.
Cikin watan na Satumba, Arsenal za ta karkare da ziyartar Brentford a wasan hamayya a gasar Premier League.
Arsenal na sa ran daukar Premier League da Europa da FA Cup da Carabawo da samun gurbin Champions League a badi.
Jerin wasa biyar da Gunners za ta yi cikin watan Satumba
Premier League Lahadi 4 ga watan Satumba
- Manchester United da Arsenal
Europa League Alhamis 8 ga watan Satumba
- FC Zurich da Arsenal
Premier League Lahadi 11 ga watan Satumba
- Arsenal da Everton
Europa League Alhamis 15 ga watan Satumba
- Arsenal da PSV Eindhoven
Premier League Lahadi 18 ga watan Satumba
- Brentford da Arsenal