Arsenal za ta yi wasa biyar cikin watan Satumba

Martin Odegaard

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta fara kakar bana da kafar dama, wadda ta hada maki 12 a wasa hudu a kakar Premier League ta 2022/23.

Cikin wasannin da ta yi ta ci kwallo 11 an zura mata biyu a raga da karawa biyu ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba.

Ranar 5 ga watan Agusta ta fara da cin Crystal Palace 2-0 a Selhurst Park, kuma Gabriel Martinelli ne ya ci mata kwallo sai Marc Guehi na Palace da ya ci gida.

Arsenal ta fara wasa a gida ranar 13 ga watan Agusta, inda ta doke Leicester City 4-2 a Emirates, Gabriel Jesus ne ya zura biyu sai Granit Xhaka da Gabriel Martinelli da kowannensu ya ci daya.

Wasa na uku kuwa Gunners zuwa ta yi ta casa Bournemouth 3-0 ranar 20 ga watan Agusta, kyaftin Martin Odegaard ne ya zura biyu a raga da kuma William Saliba.

Gabriel Jesus

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal ta ci wasa na hudu a jere ranar 27 ga watan Agusta, inda ta doke Fulham 2-1 a wasan hamayya a Emirates, Martin Odegaard da Gabriel suka samar mata maki ukun da take bukata.

Arsenal ta yi wannan gwanintar bayan da ta dauko sabbin 'yan wasa a bana ciki har da Gabriel Jesus da Zinchenko.

Gunners ta nuna cewar a shirye take ta yi gogayya da kungiyoyi kamar Liverpool da Chelsea da Tottenham da Manchester City wajen lashe Premier League a bana.

Tottenham tana cikin wadanda za a yi gwa-gwa-gwa da ita, Manchester United ma na son yin abin a zo a gani, shi ya sa take ta yin cefane.

Ranar 31 ga watan Agusta Arsenal za ta karbi bakuncin Aston Villa a wasan mako na biyar a gasar Premier League.

Aston Villa ba ta kokari sosai a kakar nan, wadda ta ci wasa daya, tana ta 15 a kasan teburi mai maki uku a wasa hudun da ta kara.

Daga nan Gunners za ta fuskanci karawa biyar a cikin watan Satumba, ciki har da fafatawa biyu a Europa League.

Wasa biyar da Arsenal za ta yi cikin watan Satumba

Arsenal za ta ziyarci Old Trafford domin fuskantar Manchester United a wasan farko cikin watan Satumba.

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Daga nan Arsenal za ta je Zurich, domin buga wasan farko a cikin rukuni da za ta kara a Europa League, bayan da ta yi ta biyar a kakar da ta wuce a teburin Premier League.

Arsenal za ta buga wasan Premier na gaba da Everton a Emirates fafatawa ta uku a cikin watan na Satumba.

Gunners za ta kara wasa na biyu a gida amma a Europa League da PSV Eindhoven.

Cikin watan na Satumba, Arsenal za ta karkare da ziyartar Brentford a wasan hamayya a gasar Premier League.

Arsenal na sa ran daukar Premier League da Europa da FA Cup da Carabawo da samun gurbin Champions League a badi.

Jerin wasa biyar da Gunners za ta yi cikin watan Satumba

Premier League Lahadi 4 ga watan Satumba        

  • Manchester United da Arsenal

Europa League Alhamis 8 ga watan Satumba       

  • FC Zurich da Arsenal

Premier League Lahadi 11 ga watan Satumba     

  • Arsenal da Everton         

Europa League Alhamis 15 ga watan Satumba    

  • Arsenal da PSV Eindhoven           

Premier League Lahadi 18 ga watan Satumba     

  • Brentford da Arsenal