Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta farko a bana da ta ci wasa uku a jere ta hau teburin Premier
Kungiyar Arsenal ta ci gaba da sa kaimi a kokarin taka rawar gani a kakar bana, inda ta doke Bournemouth da ci 3-0 ranar Asabar.
Minti biyar da fara wasa Gunners ta zura kwallo a raga ta hannun kyaftin Martin Odegaard, minti shida tsakani ya kuma kara na biyu.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Gunners ta kar na uku ta hannun William Saliba, Gabriel Jesus ya ci na hudu amma VAR ta soke, sakamkon satar gida.
Arsenal ta ci wasa uku a jere a bana, ita ce kan gaba a wannan bajintar a kakar nan, a karon farko a tarihinta tun bayan 2004/05.
Haka kuma Arsenal ta yi wasa biyu a jere a waje ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba, rabon da ta yi hakan tun 1993.
Kawo yanzu Gunners ta yi wasan Premier League 20 a jere ba canjaras ko dai ta ci ko kuma a doke ta, ba kungiyar da ke da wannan tarihin.
Bournemouth ba ta kai hari ko daya ba kafin hutu, karon farko a tarihin gasar Premier tun bayan wasan Bournemouth da Man City a Maris din 2019.
Arsenal wadda ta dare kan teburin Premier ranar Asabar za ta fafata da Fulham a wasan mako na hudu ranar 27 ga watan Agusta.
Ranar Lahadi za a buga wasa uku a karawar mako na uku tsakanin Leeds United da Chelsea, West Ham da Brighton da na Newcastle da Manchester City.
Ranar Litinin za a karkare karawar mako na uku a babbar gasar tamaula ta Ingila, inda Manchester United za ta karbi bakuncin Liverpool.
Liverpool ta yi canjaras a wasa biyu a bana da Fulham da kuma Crystal Palace.
United ta yi karawa biyu ba tare da nasara ba a hannun Brighton da kuma Brentford.