Gabriel Jesus ya ci gaba da cin Leicester kamar yadda yake yi a City

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta yi nasarar doke Leicester City da ci 4-2 a wasan mako na biyu a gasar Premier League a Emirates ranar Asabar.
Wasa na biyu a jere kenan da Gunners ta ci, bayan da ta doke Crystal Palace a karawar makon farko da ci 2-0.
Sabon dan wasan da Arsenal ta dauka a bana daga Manchester City, Gabriel Jesus shi ne ya ci biyu, karon farko da ya fara ci wa Arsenal kenan.
Dan kwallon tawagar Brazil ya ci biyu tun kan hudu ya kuma barar da damarmaki a kokarin cin uku rigis a wasan.
Jesus ya ci Leicester kwallo biyar a wasa shida a lokacin da yake Manchester City.
Granit Xhaka ya ci wa Arsenal kwallo na uku, sannan Gabriel Martinelli ya zura na hudu, na biyu jumulla da ya ci wa Arsenal a karawa biyu kenan a bana.
Leicester wadda ta yi 2-2 a wasan makon farko da Brentford a King Power ta zare daya ta hannun William Saliba, sannan James Maddison ya ci na biyu.
Arsenal ta kafa tarhin cin Leicester City karo hudu a jere ta kuma yi kan-kan-kan da bajintar da ta yi a tsakanin Fabrairun 1999 zuwa Disambar 2000.
Rabon da Leicester City ta doke Arsenal a Emirates a karawa 25 tun 1-0 a Oktoban 2020, Jamie Vardy ne ya ci kwallo.











