Arsenal ba ta taba rashin nasara a hannun Fulham a gida ba

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta doke Fulham 2-1 a wasan mako na hudu a gasar Premier League ranar Asabar a Emirates.
Kungiyoyin biyu sun je hutu ba tare da an ci kwallo ba - daga baya Fulham ta zura daya a raga ta hannun Aleksandar Mitrovic na hudu da ya ci kenan a bana.
Daga baya ne kyaftin din Arsenal, Martin Odegaard ya farke, sannan Gabriel Magalhaes ya kara na biyu.
Wasa na hudu da Arsenal ta yi nasara a jere a kakar bana kenan, tana nan a mataki na daya a kan teburi da maki 12.
Karo na 31 da Arsenal ta fuskanci Fulham a gida ba tare da rashin nasara ba a dukkan fafatawa da ta yi da kungiyar.
Wannan shi ne wasa na 100 da Mikel Arteta ya ja ragamar Arsenal a Premier League - ya yi nasara 53 da canjaras 16 da shan kashi a wasa 31.
Karo na 34 da Gunners ta fuskanci sabuwar kungiyar da ta hau Premier League tun bayan da ta yi rashin nasara a hannun Newcastle da ci 1-0 a Nuwambar 2010.
Cikin wasa 34 da Arsemal ta yi da sabbin kungiyoyin da suka hau babbar gasar tamaula ta Ingila, Gunners ta ci 29 da canjaras biyar.










