AC Milan da Ibrahimovic sun daidaita, Jesse Lingard zai koma Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta mayar da hankalinta kan sayo Jules Kounde, dan wasan baya na Sevilla mai shekara 32, bayan da Manchester City ta janye daga sayar mata da Nathan Ake. (Guardian)
Wani yunkuri da Chelsea ta yi na dauko Serge Gnabry daga Bayern Munich ma ya ci tura bayan da dan wasan gaban mai shekara 27 ya ce ya fi son yin zamansa a kungiyar ta kasar Jamus. (Football London)
Barcelona ta sanar cewa tana dab da kammala cinikin dan wasan gaban Bayern Munich din nan mai ruwan kwallaye wato Robert Lewandowski mai shekara 33. (The Athletic)
Arsenal ta ce za ta sayar da Nicolas Pepe kan kasa da fam miliyan 72 da ta sayo shi. Da alama dan wasan dan kasar Ivory Coast mai shekarra 27 ba ya cikin 'yan wasan da Arteta ke son yin aiki da su. (Diario de Sevilla - in Spanish)
Tsohon dan wasan gaba na Manchester United Jesse Lingard, mai shekara 29, ya bayyana cewa zai iya komawa Saudiyya inda aka yi masa tayin fam miliyan 10 a kowace shekara. (Daily Star)
Arsenal ta sanar cewa ta kusa cimma yarjejeniyar dauko Oleksandr Zinchenko daga Manchester City mai shekara 25. (ESPN)
AC Milan na kokarin jan hankalin Rafael Leao, dan wasan gefe dan kasar Portugal mai shekara 23, domin ya sabunta kwantiraginsa bayan da rahotanni suka ce Chelsea na shirin yin wuf da shi. (Gazetta Dello Sport - in Italian)
Everton kuwa na tattaunawa ne da Burnley domin raba ta da Mazwel Cornet mai shekara 25 bayan da aka fitar da Clarets din daga gasar Firimiyar Igila. Ya zura kwallaye tara a wasanni 26 da ya buga wa kungiyarsa. (The Athletic)
AC Milan ta kusa kammala shirin sanar da sabuwar kwatiragin da ta kulla da Zlatan Ibrahimovic, dan wasan gaba dan kasar Sweden mai shekara 40. (Football Italia)












