Nathan Ake zai ci gaba da zama a Manchester City bayan Chelsea ta kasa sayensa

Ake ya buga wa Manchester City manyan wasa 14 a kakar wasan da ta gabata

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ake ya buga wa Manchester City manyan wasa 14 a kakar wasan da ta gabata
An wallafa

Nathan Ake zai ci gaba da murza leda a Manchester City bayan Chelsea ta gaza cika sharuddan Etihad kan sayen dan wasan dan kasar Nethjerlands.

Chelsea ta dade tana tattaunawa da City kan yiwuwar daukar dan wasan mai shekara 27 a bazara.

Ake ya buga wa City manyan wasanni 14 a kakar wasan da ta wuce, inda ya zura kwallo biyu.

Ya je Chelsea lokacin yana da shekara 15 daga nan ya tafi Bournemouth, kuma daga can ne City ta saye shi a kan £40m a 2020.