Eriksen ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara uku a Man Utd

Christian Eriksen ya kwashe rabin kakar da ta wuce a Brentford

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Christian Eriksen ya kwashe rabin kakar da ta wuce a Brentford
An wallafa

Manchester United ta kammala daukar dan wasan tsakiya dan kasar Denmark Christian Eriksen.

Tsohon dan wasan na Ajax, Tottenham, Inter Milan da kuma Brentford ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara uku a Old Trafford.

"Har yanzu ina da babban burin da nake son cikawa a fagen kwallon kafa. Na san cewa akwai gagarumar gudunmawa da zan iya bayarwa, kuma wannan ne wuri mafi dacewa da ya kamata na ci gaba da gudanar da rayuwata ta kwallon kafa," a cewar Eriksen, mai shekara 30.

"Manchester United kungiya ce ta musamman, kuma na zaku na soma murza leda a can."

A farkon watan Yuli, Eriksen ya amince ya sanya hannu kan yarjejeniyar aiki da United bayan ya kammala zaman takaitaccen lokaci a Brentford wanda ya kare a watan Yuni.

Shi ne dan wasa na biyu da United ta saya a karkashin jagorancin sabon koci Erik ten Hag bayan dan wasan Netherlands Tyrell Malacia wanda ta sayo daga Feyenoord.

Eriksen ya ci kwallo 52 sannan ya taimaka aka zura kwallo 66 a wasanni 237 na Gasar Firimiya da ya buga wa Tottenham da Brentford.