Mece ce huciyar zazzaɓi?

Asalin hoton, Getty Images
Huciyar zazzaɓi ko "Herpes labialis", cuta ce da likitoci suka bayyana ake kamuwa da ita daga wata ƙwayar cuta da ake kira "Herpes simlex virus."
Tana yaɗuwa kamar sauran ƙwayoyin cututtuka na virus da ake yaɗawa da hanyar jima’i, ko wajen ƙarin jini, ko wajen sumba.
Cutar huciyar zazzaɓi kan shafi leɓe ko gefen bakin mutum da ke haddasa wasu ƙuraje masu ruwa ko maruru masu tsananin zafi da raɗaɗi.
A lokacin matakin farko na yaɗuwar ƙwayar cutar, ta kan shiga jikin fata ko ruwan jikin mutum inda ta kan riƙa yaduwa.
A tattaunawarsu da BBC, Dakta Ahmad Tijjani Ibrahim na babban Asibiti da ke garin Babura a jihar Jigawa arewacin Najeriya, ya ce cutar na bayyana ne da fesowar wasu ƙananan ƙuraje ko maruru, galibi a gefen leɓen bakin mutum.
"Ƙurajen masu ruwa ko maruru kan fito a leɓen ƙasa ko na sama da kan sa leɓɓan su kumbura, kuma sauran alamomi kamar su zazzabi kan bayyana, duk da cewa a wasu lokuta ba sa nuna wasu alamomi,’’ in ji Dakta Tijjani.
‘’Suna kuma da zafi da zogi sosai’’.
A cewar likitan, bayan wannan ƙwayar cuta ta herpes da ke haddasa cutar huciyar zazzabin ta samu damar shiga jikin dan adam, ta kan zauna a jikin mutum ta yi likimo, ta yadda mutum ba zai taba ganewa yana dauke da ita ba, wani ma har ya gama rayuwarsa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Abinda yake tashin wannan cutar har ya zo da alamominta shi ne idan mutum ya yi zazzabi mai zafi, yana iya tayar da cutar daga barci, ta yadda za ta iya fito da alamominta, in ji shi.
Har ila yau a cewar Dakta Tijjani, ko yaya garkuwar jikin mutum ta yi kasa, wannan ƙwayar cutar kan samu wata dama da za ta bayyana kanta, shi yasa yawanci ake ganin huciyar a lokacin da aka yi zazzabin maleriya.
"Lokacin da cutar ta shiga jikin mutum, alamominta na iya yin kama da na cutar maleriya, kamar su zazzabi, da ciwon kai, da kasala, da ciwon gabobi, da maruru na baki,’’ in ji shi.
Amma kuma in ji shi ba dole ba ne a ce sai ka yi zazzabi ne sannan cutar za ta bayyana, idan mutum ya ga wannan kumburin ba tare da ya yi wani zazzabi ba, to bai dade da kamuwa da cutar ba.
Abin da ya kamata mutum ya yi shi ne ya tafi asibiti don a ba shi magugunan zafin jiki, wanda dama shi ke tayar da cutar, don idan da riga ta shiga jikin mutum ba ta fita.
Yawanci cutar ba ta wuce kwanaki goma ta ke warkewa. Amma dai ƙwayar cutar tana jikin mutum.
‘’Idan suka fito sukan rika yin zafi tare saka ciwon kai a wasu lokuta ma har da zazzabi, shi yasa ake cewa hucewar zazzabin’’.
Alamomin cutar
Ba kasafai cutar ke bayyana alamominta ba nan take bayan kamuwa da kwayar cutar ta herpes simplex virus, kana yawanci ta kan bayyana ne a cikin makonni uku da kamuwa da ita.
Yawanci wadanda suka kamu su kan riga jin radadi da zogi a wuraren bakinsu, wanda daga bisani kuraje kan feso a leben kasa.
Zazzabi, da bushewar makogwaro, da jin zafi wajen hadiyar abinci ko ruwa, da kuma ciwon jijiyoyi.
- Jajayen kuraje masu ruwa
- Kuraje masu yawa da kan hade su girma tare wuri guda su zama daya babba
- Kananan kurajen masu dauke da mugunya mai launin rawaya.
Hanyoyin kamuwa
A cewar Dakta Tijjani, da zarar mugunya ko jinin da ke fita daga jikin kurajen da suka yi mararu suka taba jikin ko ya shiga jikin wanda ba shi da cutar, yana iya dauka,’’ in ji daktar Tijjani.
Ya kume ce don haka:
Mutum zai iya kamuwa da huciyar zazzabi ta hanyar mu’amala da wanda ke dauke da cutar – kamar sumbanta ko jima’i.
Ta hanyar kusanci ko shafar fatar wanda ke dauke da cutar, ko amfani da wani abu nasa kamar su brush ko cokali ko tawul ko kofin shan ruwa ko shayi.
Akwai yiwuwar mace mai juna biyu ko mai shayarwa yada wa jaririn da ke cikita ko wanda ta ke goyo.
Karyewar garkuwar jikin dan adama wacce ke bas hi kariya daga kamuwa da kwayoyin cutar.
Kariya
Masana sun bayyana cewa duk da cewa wannan cuta da hucewar zazzabi kan jima a jikin mutum ba tare da ya sani ba, har sai ta bayyana kanta.
Akwai kuma hanyoyin da suka kamata mutane su rika bi don kiyaye kamuwa da ita musamman daga wanda ya riga yake dauke da ita.
Dakta Ahmed Tijjani Ibrahim ya bayyana cewa ya kamata mutane su guje wa duka hanyoyin da ya bayyana cewa suna haifar da yaduwar cutar daga wanda ke dauke da ita zuwa mai lafiya.
‘’Muddin dai mutum zai guji amfani da duk wani abubuwan da wanda ke dauke da cutar ke amfani da su kamar so cokali da kwano da kofin cin abinci, zai kare shi daga kamuwa,’’ in ji shi.
Yawanci da yake ba a sani mutum na dauke da cutar hucewar zazzabin idan ba an ga fesowar kurajen ba, yana da matukar wahala a kauce wa yaduwarta cikin sauki.
Amma kuma mutum ya tabbatar da cewa garkuwar jikinsa na da karfi a koda yaushe’’.
Abu mafi muhimmanci in ji Dakta Tijjani dai shi ne da zarar cutar ta bayyana ko kuma mutum ya san yana dauke da cutar sai ya yi sauri a garzaya asibiti don neman magani.












