Dalilan da Kano Pillars ta fadi daga Firimiyar Najeriya a bana

Kano Pillars

Asalin hoton, NPFL Twitter

An wallafa

Ta tabbata cewar Kano Pillars ta fadi daga gasar Firimiyar Najeriya bana a karo na uku a tarihin kungiyar.

Tun farko kungiyar da aka kafa a 1990 ta fadi daga gasar Firimiyar kasar a shekarar 1994 da 1999.

Kungiyar da ake kira sai masu gida wadda ta lashe kofin babbar gasar tamula ta Najeriya karo hudu ba za ta buga kakar da za a yi ta 2022/23 ba.

Kungiyar tana da dadadden tarihi a fagen taka leda a kasar da Afirka, wadda ta samar da fitattun 'yan wasa masu magoya baya da yawa.

To ko wadanne dalilan ne suka sa Pillars ta ci karo da koma baya haka?

Shugaban marubuta labarin wasannin kasa reshen jihar Kano, Zaharadden Saleh ya yi karin bayani kan abubuwan da suka ja kungiyar ta fadi a kakar bana.

Bayanan bidiyo, Sharhi kan dalilan da Kano Pillars ta fadi daga Firimiyar Najeriya

Shugabancin Surajo Yahaya Jambul:

A shekarar 2019 gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada Surajo Shu'aibu Yahaya da ake kira Jamul a matakin shugaban Kano Pillars.

Tun bayan da aka nada Jambul shugabanci wasu suka fara korafin cewar bai da kwarewar jan ragamar babbar kungiyar kamar Pillars.

Wasu ma na ganin bai kamata tun farko a sauya Alhaji Tukur Babangida, wanda ya goge a sanin tamaular Najeriya da kwarewa da gogewa ba.

Jambul ya karbi kungiyar daf da za ta dauki Aiteo Cup da yin ta biyu a kakar da aka kammala a lokacin.

To sai dai a kakar ya ja ragamar kungiyar ta yi vi ban kwana da gasar kofin Zakarun Afirka wato Champions League, inda Ashanti Kotoko ta Ghana ta yi nasara a kan Pillars 5-2 gida da waje.

Haka kuma a kakar gaba a yi waje da Pillars a Confederation Cup, kuma wata karamar kungiya ta Senegal mai suna Jaraaf, wadda ta ci 3-1 gida da waje.

Bayan kasa taka rawar gani a wasannin zakarun Afirka, Pillars ta ci gaba da rashin kokari a wasannin da take buga wa a Firimiya.

Kyaftin Rabia Ali

Asalin hoton, Kano Pillars

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rashin sakin kudi daga gwamnati

Gwamnatin jihar Kano ta janye daga bai wa Kano Pillars kudi kamar yadda aka saba yi, in banda albashin 'yan wasa.

'Yan kwallon suka koma ba sa samun ladan wasa da sauran kudaden da ke kara karsashin 'yan kwallo domin suke saka kwazo.

Sai dai wasu sunce gwamnatin ko ta bayar da kudi kwalliya ba ta biyan kudin sabulu, saboda rashin kwarewar shugabanci.

Pillars ta buga wasanninta na gida a waje

Sai masu gida ta koma buga wasa a Kaduna, filin da ake kira Ahmadu Bello daga nan ta koma karawa a Katsina, filin wasa na Muhammadu Dikko.

Daga nan ta koma wasa a Kano nan da nan kungiyar ta yi laifin da aka dauke ta zuwa Abuja, filin MKO Abiola na babban birnin tarayyar Najeriya.

Daga nan kuma Pillars ta koma buga wasanninta a Sani Abacha da ke kofar mata.

A dai kakar bana da Pillars ke fatan hada maki sai kungiyar ta ci karo da koma bayan da aka ci gaba da zargin Jambul da rashin iya gudanar da mulki.

Matsi ya ci gaba da hawan shugaban, wanda magoya baya suke ta shakkun da kyar idan kungiyar ba ta yi abin kunya ba.

Kwashe maki shida daga Pillars

Bayan da aka dawo da Kano Pillars buga wasa a gida wato filin wasa na Sani Abacha, an samu yamutsin fasa motar Katsina United cikin watan Afirilu.

An kara kwashe maki uku daga Kano Pillars kan laifin da Jambul ya aikata a karawa da Dakkada.

Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Najeriya, LMC ta dakatar da shugaban Kano Pillars, Suraj Yahaya daga shiga harkokin wasanninta nan take.

Hukumar ta fitar da wani jawabi a karshen mako da ya shafi dakatar da shugaban da wasu karin hukunce-hukunce.

An tuhumi Kano Pillars da karya doka ta gudanar da wasannin Firimiya a lokacin da ta buga karawa da Dakkada ranar 23 ga watan Yunin 2022.

Magoya baya sun taka rawar gani wajen faduwar Pillars

Kungiyar magoya bayan Kano Pillars mai dunbin magoya ta bayar da gudunmawa wajen faduwar Pillars daga gasar Firimiyar Najeriya a bana.

Magoya bayan sun kasa nuna halin da'a a wasannin da ta buga a Kaduna da Katsina, wanda hukumar gudanar da gasar ta Najeriya ke ta gargadinsu.

Maganar rikici da tayar da yamutsi ba abun da yake kawo ci gaba ba ne a kungiyar, amma magoya bayan Pillars sun yi suna a rashin hakuri a lokacin taka leda.

'Yan wasan da Pillars ta dauka

Ana ganin cewar Pillars ba ta dauki 'yan wasan da suka da ce ba musamman a kakar nan, idan ba haka ba ya kamata su fahimci cewar sana'arsu ce ba wanda zai kama musu sai dai kwazonsu.

To sai dai kuma rashin samun kudi a kan kari ya taka rawar gani da 'yan kwallon suka kasa sa kwazo a wasanninsu, ga tarin matsaloli.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Bayan da abubuwa suka yi lalacewar da ba damar gyara, shi ne aka kori Surajo Shu'aibu Yahaya aka nada Alhaji Ibrahim Galadima na rikon kwarya.

Pillars ta karkare a mataki na 19 da maki 45, bayan da ta ci wasa tara da canjaras rata aka doke ta karawa 20.

Haka kuma an zura kwallo 50 a ragar Pillars, ita kuma ta ci 26 a kakar bana da hakan ya sa ta yi ban kwana da babbar gasar tamaula ta Najeriya da aka karkare.

To sai dai kuma wasu na cewar watakila Pillars ta buga gasar nan gaba, bayan da kungiyar Gombe mai suna Doma United ta samu gurbin shiga gasar kaka mai zuwa, amma wasu na cewar za ta sayar da gurbin ne.

An ce kungiyar ta Gombe na neman naira miliyan 250 daga Kano Pillars, sai su yi musaya, masu gida ta koma Firimiya ita kuwa Doma ta ci gaba da buga rukuni na biyu.

Ba wannan karon bane ake cinikin gurbi a babbar gasar tamaula ta Najeriya, domin Kwara ta yi haka a 2019, haka itama Delta ta sayi gurbi a wajen Kada City.

 Saboda haka wasu na ganin ya kamata a kawo sayen gurbi tsakanin kungiyoyi idan har ana son gasar ta yi armashi.

Ya kamata a kafa dokar da za ta samar da fitattun kungiyoyin da za su ke wakiltar kasar a wasannin waje domin kai wa gurbin da ya kamata.

Nasarorin da Pillars ta samu:

Nigerian Firmiya League

Zakaru karo hudu a 2007–08 da 2011–12 da 2013 da kuma 2014

Ta kuma yi na biyu a 2009–10.

Kofin kalubalen Najeriya

Zakaru a karo biyu a 1953 da 2019

Sai na biyu karo biyu a 1991 da 2018

Nigerian Super Cup

Zakara karo daya 2008

Kwazon da ta yi a wasannin zakarun Afirka

Ta buga gasar karo shida

2009 – wasan daf da karshe

2011 – zagayen farko

2013 – zagayen farko

2014 – wasan neman gurbi

2015 – zagayen farko

2020 – wasan neman gurbi