Ziyarar Yarima Harry da bikin al'ada cikin hotunan Afirka

An wallafa

Zaɓaɓɓun ƙayattun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata

A fisherman walks towards his catch on a beach

Asalin hoton, FEISAL OMAR/REUTERS

Bayanan hoto, Wani mai sana'ar kama kifi kenan a lokacin da ya nufo inda babban kifin da ya kamo yake, a babban birnin ƙasar Somaliya, Mogadishu a ranar Litinin.
 traditional Tanoura folk dance

Asalin hoton, MOHAMED ELSHAHED/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Yadda aka yi rawar al'ada ta Tanoura a lokacin bikin al'ada na shekara-shekara a birnin Ismailia dake gabashin ƙasar Masar a ranar Litinin.
apricot-harvesting season in Egypt’s Qalyubia province

Asalin hoton, MOHAMED ABD EL GHANY/REUTERS

Bayanan hoto, Wata manomiya a lardin Qalyubia na ƙasar Masar, a yayin da take tsinkar ƴa'ƴan itatuwan da ta shuka a ranar Litinin.
a boy hanging out with camels in Chad’s capital

Asalin hoton, ISSOUF SANOGO/AFP

Bayanan hoto, Wani yaro kenan ke shan mangoro a tsakiyar raƙuma a N’Djamena, babban birnin ƙasar Chadi.
Fans of Meghan, the Duchess of Sussex

Asalin hoton, EMMANUEL OSODI/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Wasu mata masoyan Gimbiya Meghan ke ɗaukar hoto da ita a ranar Asabar, yayin da ita da mijinta Yarima Harry suka halarci wasan kwallon mata ta volleyball a babban birnin Najeriya, Abuja.
The royal couple were in the West African nation

Asalin hoton, AKINTUNDE AKINLEYE/REUTERS

Bayanan hoto, Yarima Harry da matarsa Gimbiya Meghan, a birnin Lagos na Najeriya a wajen wasan ƙwallon kwando a ranar Lahadi.
A boy gets a haircut on Wednesday in a camp in Gedaref in eastern Sudan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An yi wa wani yaro aski a sansanin ƴangudun hijira na Gedaref da ke gabashin Sudan. Rikicin Sudan da ya ɓarke a watan Afrilun 2023 ya yi sanadin raba mutane da dama da muhallansu.
upils in Kenya’s capital, Nairobi, head back to school

Asalin hoton, DONWILSON ODHIAMBO/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ranar Litinin a lokacin da ɗalibai suka taso daga makaranta a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya, makonni bayan da ƙasar ta yi fama da ambaliyar ruwa.