Najeriya za ta fafata da Algeria a wasan sada zumunta

Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta na Oran, domin buga wasan sada zumunta da Algeria ranar Talata.

Super Eagles ta sauka a Algeria tun a makon jiya, inda ta zauna a Constantine, wadda ta buga wasan sada zumunta da tawagar Algeria, wadda za ta buga CHAN a bana.

Sun kuma tashi wasan 2-2 da suka fafata ranar Juma;a, inda Alex Iwobi da kuma Cyriel Dessers suka ci wa Najeriya kwallayen.

Tawagogin biyu za su kece raini a yammacin Talata a filin wasa na Stade Olympique d’ Oran.

Algeria da Najeriya sun kai zagayen karawar karshe ta neman shiga gasar kofin duniya a bana, inda Kamaru ta cire Algeria, Ghana ta yi wa Super Eagles fancale.

Ranar Juma'a Algeria ta buga wasan sada zumunta da Guinea, inda ta yi nasara da ci 1-0.

Karo na hudu da Algeria ta yi nasara a jere, ita kuwa Najeriya karkashin Jose Peseiro na sa ran yin nasara ta uku.

Kungiyoyin biyu sun fafafata sau 21 a tsakaninsu, kowacce ta ci tara da canjaras uku.

Canjaras na baya da suka yi shi ne a 1993 - daga lokacin Super Eagles ta ci wasa shida daga tara.

Algeria ta doke Super Eagles a kofin Afirka a Masar a 2019 da kuma a wasan sada zumunta a 2020 a Austria.

Najeriya na fama da 'yan wasan da ke jinya da suka hada da Victor Osimhen da Umar Sadiq da kyaftin Ahmed Musa.

Tuni kuma Wilfred Ndidi da William Troost-Ekong suka bar sansanin 'yan wasa suka koma Ingila, don yin jinya.