PSG na son Rashford da Diaz don maye gurbin Mbappe, Arsenal na neman gola

Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germain na shirin taya Marcus Rashford fam miliyan 80, kuma kungiyar ta ce a shirye take ta rika biyan dan gaban na Manchester United da Ingila albashin kusan fam dubu 500 a mako. (Star)
Haka kuma PSG din na son dan wasan gaba na gefe na Liverpool kuma dan Colombia Luis Diaz, mai shekara 27 domin maye gurbin Kylian Mbappe, wanda ake sa ran zai tafi Real Madrid. (El Pais )
A shirye shugaban Chelsea Todd Boehly yake ya sayar da Romelu Lukaku, wanda ke zaman aro a Roma, da kuma mai tsaron ragar Sifaniya Kepa Arrizabalaga, wanda shi kuma yake zaman aro a Real Madrid, ga kungiyoyin gasar Saudiyya a bazara domin samun fam miliyan 100 daga cinikin 'yanwasa. (Talksport)
Masu nema wa Manchester United 'yanwasa sun fara rangadin manyan kungiyoyin Turai, kafin bude kasuwar saye da sayar da 'yanwasa, domin ta san 'yanwasan da za ta saya tun da wuri a bazaran nan. (ESPN)
Manchester United ta sa sayen babban dan baya ya kasance abin da ta ba fifiko a bazarar da ke tafe, inda ta sa dan bayan Juventus da Brazil Gleison Bremer, mai shekara 26, tare da dan bayan Everton kuma dan Ingila Jarrad Branthwaite mai shekara 21 cikin wadanda ta fi so. (i Sport)
Brighton na fargaba cewa mai horad da 'yanwasanta Roberto de Zerbi zai bar kungiyar a bazara saboda Barcelona, da Chelsea da Liverpool na harin kociyan dan Italiya.(Times )
Dan bayan Liverpool Joe Gomez, da dangaban Brentford Ivan Toney, da kuma golan Rangers Jack Butland, za su kasance cikin tawagar Ingila da za ta kara da Brazil da Belgium a wasannin sada zumunta na watan Maris. (Sky Sports)
Watakila Paris St-Germain ta bayar da matashin danwasanta na tsakiya na Netherlands Xavi Simons, mai shekara 20, wanda ke zaman aro a RB Leipzig, domin musaya da Bernardo Silva na Manchester City da Portugal. (CaughtOffside)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Barcelona za ta iya sayar da, danbayanta Ronald Araujo, na Uruguay, wanda ake danganta shi da tafiya Bayern Munich, idna har ta samu tayin da ya kai yuro miliyan 100. (ESPN)
Shugaban Inter Milan Giuseppe Marotta ba ya tsammanin wata matsala daga dangaban sa na Argentina Lautaro Martinez, a kan tsawaita kwantiagin danwasan mai shekara 26, a kungiyar ta Serie A. (Gazzetta dello Sport )
Arsenal na sa ido a kan golan Columbus Crew da kuma tawagar Amurka Patrick Schulte, mai shekara 23, idan har Aaron Ramsdale,ya yanke shawarar barin kungiyar a bazaran nan. (Telegraph )
Watakila Chelsea ta saye matashin danwasan tsakiya na Bayern Munich, idan kungiyar ta Bundesliga ta yanke shawarar sayar da danwasan na Jamus, wanda ake ganin za ta sayar da shi fam miliyan 80 kuma Manchester City da Liverpool na sha'awar matashin mai shekara 21. (Mail)
Chelsea ta cimma yarjejeniya da Brentford domin Bernardo Cueva ya zama kociyanta daga karshen kakar nan. (Athletic )
Southampton za ta yi kokarin sayen Matias Soule na Argentina dagaJuventus idan ta yi nasarar tsallakawa zuwa gasar Premier, yayin da su ma Crystal Palace, da Newcastle United da Aston Villa ke sha'awar dangaban mai shekara 20. (Calciomercato)














