Al-Hilal ta zama ta farko da ta kafa tarihin yawan cin wasa a jere

Al Hilal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kungiyar Saudi Arabiya, Al-Hilal ta zama ta farko da ta kafa tarihin cin wasa da yawa a jere, bayan da ta doke Al-Ittihad 2-0 a Champions League na Asia.

Wasa na 28 a jere kenan da kungiyar ta yi nasara jimilla da ba mai wannan tarihin.

Wadda ke rike da bajintar a baya ita ce wata kungiya a Wales, The New Saints a 2016 wadda ta yi nasarar cin wasa 27 a jere.

Al-Hilal, wadda take da fitattun 'yan wasa ciki har da tsohon dan kwallon Fulham, Aleksandar Mitrovic ta ci wasa 28 a jere tun daga 1-1 da Damac ranar 21 ga watan Satumba.

Shima tsohon dan wasan Wolves, Ruben Neves na buga wa Al-Hilal tamaula har da dan kwallon Brazil, Neymar, wanda ya koma kungiyar daga Paris St-Germain kan (£77.6m) har da tsarabe-tsarabe.

Koda yake Neymar na jinya tun raunin da ya ji a cikin watan Oktoba.

Al-Hilal, wadda tsohon kociyan Benfica da Flamengo, Jorge Jesus ke jan ragama tana ta dayan teburi a babbar gasar tamaula ta Saudi Arabiya ta bana.

Ta kuma bai wa bai wa kungiyar da Cristiano Ronaldo ke taka leda Al-Nassr tazarar maki 12.

Mitrovic ya ci kwallo 26 daga 81 da Al-Hilal ta zura a raga a wasa 28 da ta yi nasara a jere.

Ta lashe wasa 16 a lik da uku a wasannin cikin gida da kuma tara a Champions League na Asia.

Nasarar da Al-Hilal ta yi ranar Talata ya sa ta ci kwallo 4-0 gida da waje ta kuma kai daf da karshe a gasar zakarun Turai ta Asia.