Kocin Lazio Sarri ya jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda

Maurizio Sarri

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kocin Lazio, Maurizio Sarri ya ajiye aikin jan ragamar kungiyar, bayan rashin nasara biyar daga karawa shida a dukkan fafatawa.

Ranar Litinin Udinese ta doke Lazio 2-1 a Serie A, hakan ya sa kungiyar tana ta tara a teburi da tazarar maki bakwai tsakaninta da gurbin shiga gasar zakarun Turai.

A makon jiya Bayern Munich ta yi waje da Lazio daga Champions League.

Sarri, mai shekara 65 ya koma Lazio a 2021, wanda ya kai kungiyar mataki na biyu a Serie A kakar da ta wuce.

Kwazon da kungiyar ta yi mafi girma tun bayan lashe kofin babbar gasar tamaula ta Italiya a 1999-2000.

Tuni kungiyar ta nada mataimakinsa, Giovanni Martusciello a matakin kociyan rikon kwarya.

Lazio za ta ziyarci Frosinone, wadda take ta ukun karshe teburi ranar Asabar a Serie A, za kuma ta fafata da Juventus gida da waje da Juventus a daf da karshe a watan gobe a Italian Cup.

Sarri ya yi kaka daya a Chelsea ia 2018-19, wanda ya lashe Europa League da kai kungiyar mataki na uku a teburin Premier League da zuwa wasan karshe a Carabao Cup.

Kafin zuwa Chelsea, Sarri ya horar da Napoli, wadda ya kai mataki na biyu a teburin Serie A karo biyu, shi ne fitaccen mai horar wa a Serie A a kakar 2016/17.

Ya kuma lashe babban kofin tamaula na Italiya tare da Juventus a 2019-20.