Wace ce Stormy Daniels - matar da ta zame wa Trump ƙarfen-kafa?

Kotu a birnin New York na Amurka ta samu tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da laifi a zargin da ake masa na biyan kuɗi domin ɓoye alaƙar da ke tsakaninsa da wata ƴar fim ɗin batsa.
Ana zargin Trump ne da biyan kuɗi ga matar mai suna Stormy Daniels gabanin zaɓen 2016 domin ta rufe bakinta kan alaƙar da ta wanzu tsakaninsu.
Ita dai Stormy Daniels ta ce Trump ya taɓa neman ta a 2006, shekara ɗaya bayan ya auri Melania Trump.
Kuma hakan ya faru ne kimanin shekaru 10 kafin Donald Trump, wanda ɗan kasuwa ne, ya hau kan shugabancin Amurka.
Trump dai ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, kuma ya ce an biya ta kuɗi ne domin hana ta yi masa ƙazafi da nufin tatsar kuɗi daga gare shi.
Wace ce Stormy?
Sunan Stormy Daniels na ainahi shi ne Stephanie Clifford.
Tana da shekara 44 a duniya, kuma ta fito ne daga birnin Baton Rouge na jihar Louisiana da ke ƙasar Amurka.
Daniels ta shahara a tsawon shekara 20, saboda sana’arta ta fina-finan batsa.
Takan taka rawa a wasu fina-finan, sannan ta bayar da umurni a wasu.
Ta ce an haɗa ta da Trump ne a watan Yulin 2006 lokacin wata gasar ƙwallon golf.
A ranar 28 ga watan Oktoban 2016, jim kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasa da Trump ya yi nasara, Daniels ta sa hannu kan wata yarjejeniyar cewa za ta yi gum da bakinta game da alaƙar da ta wanzu tsakaninta da Donald Trump.
Inda aka biya ta dalar Amurka 130,000, kamar yadda takardun da aka gabatar wa kotu suka nuna.
Lauyan Stormy a wancan lokacin, Keith Davidson da lauyan Trump, Michael Cohen ne suka sa hannu a kan yarjejeniyar.
Akwai wurin da aka ware a jikin takardar inda Trump zai sa hannu, sai dai bai yi hakan ba.
End of Ƙarin labaran da za ku so karantawa:
Yadda rikicin ya fara
A 2018 ne, Stormy Daniels ta shigar da ƙara tana zargin Trump da ɓata mata suna bayan ya sanya wani bayani a shafinsa na tuwita, inda ya zarge ta da damfara saboda ta ce ana mata barazana game da yiwuwar za ta fallasa aikin baɗala da ya faru tsakaninta da shi.
Daga baya kotu ta wanke Trump, inda ta ce kalaman Trump a kan Daniels ba na ɓata suna ba ne, kuma sun yi daidai da tanadin tsarin mulkin ƙasar na 'yancin faɗar albarkacin baki.
Daniels ta ce wani mutum ne ya tunkare ta lokacin da take tare da 'yarta a wurin ajiye motoci na Las Vegas cikin shekara ta 2011, inda ya yi mata barazana, bayan ta amince za ta bayyana alaƙarta da Trump a wata tattaunawa ta talbijin.











