Gane Mini Hanya kan Lamunin Karatu na Najeriya 02/11/2024

Bayanan sautiLatsa hoton sama domin saurare
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumomin Najeriya sun ce zuwa yanzu ɗaliban jami'a da sauran manyan makarantu fiye da 40,000 ne suka ci gajiyar sabon tsarin ba da lamunin karatu na gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Dama dai gwamnatin ta ce ta ɓullo da shirin bashin karatu ne don ganin babu wani ɗan Nijeriya da aka tsame wajen samun ilmi mai inganci.

An ɓullo da shirin ne bayan jami'o'in Najeriya sun ninninka kuɗin rijistar karatu, lamarin da suka alaƙanta da rashin samun isassun kuɗaɗen gudanarwa daga hukumomi.

A filinmu na Gane Mani Hanya na makon nan, mun tattauna da wani babban jami'i a hukumar ba da lamunin karatu ta ƙasar (NELFUND), Umar Mukhtar.