Waiwaye: Gargaɗin jabun kuɗi da neman biyan diyya kan kisan masu Maulidi a Kaduna
Wannan maƙala na ɗauke da wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata.
Ku yi hankali da jabun takardun naira a hannun jama'a - CBN

Asalin hoton, State House
Babban Bankin Najeriya, CBN, ya sanar da bankuna da ‘yan Najeriya cewa su yi hattara da jabun takardun naira musamman kudaden da ake kashewa a wuraren sayar da abinci da sauran cibiyoyin kasuwanci a kasar.
A cewar Babban Bankin, laifi ne da za a iya yanke wa mutum hukuncin dauri a gidan yari idan aka kama shi da jabun takardun kuɗin.
Babban Bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a.
CBN ya ci gaba da cewa, “An jawo hankalin CBN kan yadda wasu mutane ke yawo da jabun takardun kudi, a kasuwannin sayar da kayan abinci da cibiyoyin kasuwanci a manyan biranen kasar nan.“
Don kauce wa shakku, sashe na 20 (4) na dokar Babban Bankin (2007) da aka yi wa kwaskwarima, ya bayyana karara cewa amfani da jabun takardun kuɗi a hannun jama'a ko kasuwanni a Najeriya laifi ne da za a yanke hukuncin dauri mafi karanci na shekaru biyar.
“CBN na ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro domin kwace irin waɗannan jabun takardun kudin Naira da kuma gurfanar da masu su a kotu.“
Haka kuma ana kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda ake zargi yana da jabun takardun naira zuwa ga hukumomi.
Manyan mutanen da suka yi magana kan jefa wa fararen hula bam a Kaduna

Al'umma da ƴan siyasa da ƙungiyoyin addinin musulunci a Najeriya suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu bayan harin da sojoji suka kai "bisa kuskure" a Tudun Biri, wani ƙauye a ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna a arewacin ƙasar.
Harin dai ya yi sanadin asarar rayuka da dama tare da jikkatar wasu da ke samun kulawa a asibiti.
Hukumomi sun bayyana cewa mutane 85 ne harin ya kashe, sai dai ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma al'ummar ƙauyen na cewa adadin ya zarce haka.
Babban hafsan sojin Najeriya ya nemi afuwar al'ummar Tudun Biri

Asalin hoton, Nigerian Army
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Janar Taoreed Lagbaja ya nemi afuwa daga al'ummar ƙauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna, kan wani harin jirgin maras matuƙi da ya kashe mutane a ranar Lahadi.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Litinin, ta bayyana cewa Janar Lagbaja ya kai ziyarar jaje a ƙauyen yau Talata inda "ya nuna nadama game da mummunan lamarin."
Janar Lagbaja ya ce lamarin ya faru ne yayin da dakarun sama na ƙasar ke gudanar da wani sintiri ta sama, inda suka tsinkayi gungun mutane "waɗanda suka yi kuskuren fassara abubuwan da suke yi" a matsayin tamkar irin na ƴan fashi, wanda hakan ya sa aka kai musu hari.
Ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike domin "gano inda aka samu naƙasun da ya haifar da wannan mummunan abu," inda za a yi amfani da sakamakon binciken domin daƙile faruwar irin hakan a gaba.
Al'ummar Najeriya da dama sun nuna fusata kan lamarin, wanda shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kai.
Tuni dai hukumar agajin gaggawa ta ƙasa ta bayyana cewa mutum 85 ne suka rasu sanadiyyar harin, yayin da wasu mutanen 60 suka samu rauni, sai dai ƙungiyoyin masu kare hakkin bil'adama na ganin cewa alƙaluman sun zarce haka.
An dai samu irin wannan kuskure a baya, inda hare-haren na sojojin Najeriya ke shafar fararen hula.
Sojojin Najeriya sun kama jirgin ruwa ɗauke da gangar mai fiye da 3,000 na sata

Asalin hoton, AFP
Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta kama wani jirgin ruwa ɗauke da gangar mai 3,665 da take zargi na sata ne a yankin Igbokoda na jihar Ondo.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ta kama ma'aikatan jirgin 17, da take zargi da satar man daga rijiyar mai ta Ebesan a ƙaramar hukumar Ilaje da ke jihar.
Daraktan yaɗa labaran rundunar, Commodore Ayo-Vaughan, ya ce an kama jirgin ne a ranar Alhamis.
Ya ce rundunar ta samu bayanan sirri kan ayyukan mutanen da take zargi da sace man, inda nan take ta tura jami'anta waɗanda suka yi nasarar kama mutanen.
Sanarwar ta ce sojojin sun gano cewa an daɗe ana amfani da jirgin wajen satar man daga kowane ɓangare na rijiyar.
Jirgin na da girman da zai iya ɗaukar nauyin metric ton 15,000, kuma a lokacin da aka kama shi yana ɗauke da man da nauyinsa ya kai metric ton 500.
Satar mai a kudancin Najeriya dai wata matsala ce da ta daɗe tana ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya, inda ɓata-gari ke sace ɗimbin mai ta hanyar fasa bututan man ko amfani da rijiyoyin mai ba bisa ƙa'ida ba, lamarin da ke ƙara haifar da koma-baya kan tattalin arzikin ƙasar.
An ɗaure ɗan Najeriyan da ya damfari mutanen ƙasashe 13

Asalin hoton, EFCC
Wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya ta samu wani mazambaci, Eze Harrison Arinze, da laifin damfarar mutum 34 a ƙasashe 13 kuɗin da ya kai $592,000.
Waɗanda ya damfara sun fito daga Burundi da Kamaru da Coasta Rica da Jamus da Ghana da Hungary da India da Rwanda da Singapore da Afirka ta Kudu da Uganda da Amurka da Zimbabwe.
Hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati, EFCC ce ta gurfanar da Arinze gaban mai shari'a J.K Omotosho kan laifin da ya shafi yin sojan-gona.
Arinze dai ya amsa laifinsa bayan da aka karanto masa uhumar da ake yi masa.
Lauyan mai gabatar da ƙara Christopher Mshelia ya nemi kotu ta yanke wa wanda ake tuhuma hukunci.
Mai shari'a Omotosho ya yanke wa Arinze hukuncin shekara uku a gidan yari da zaɓin biyan tara ta naira miliyan 3.
A baya-bayan nan, Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya ce abin damuwa ne yadda kashi 70 cikin 100 na ɗaliban Najeriya ke aikata zamba ta intanet.
Najeriya da Kuwait sun ƙulla yarjejeniyar fara zirga-zirgar jiragen sama

Asalin hoton, X/Keyamo
Gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniya da ƙasar Kuwait don fara zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin ƙasashen biyu.
Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Mista Keyamo ya ce ya rattaɓa hannu a madadin gwamnatin Najeriya don cimma yarjejeniyar jigilar jiragen sama tsakanin ƙasashe biyu, don bayar da dama ga kamfanonin jiragen sama da aka keɓe don gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci, wanda ya shafi jigilar fasinjoji da kaya.
A cewar Keyamo, an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a taron tattaunawa kan harkokin sufurin jiragen sama na ƙasashen duniya (ICAN) da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasashen duniya (ICAO) ta shirya a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.
“Wannan zai bunƙasa harkokin kasuwanci da yawon bude ido da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Ni da tawagata za mu ci gaba da tattaunawa kan hanyoyi daban-daban tare da ƙasashe daban-daban da ke nan don halartar wannan taron na ICAO na shekara-shekara har zuwa karshen mako, '' in ji Keyamo.
Ko sabon taron dangin jam’iyyun adawa zai tayar da hankalin APC?

Asalin hoton, Facebook/Rabiu Kwankwaso
A baya-bayan nan ne Jam'iyyun hamayya bakwai a Najeriya ciki har da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP suka ɗauki matakin yin gamin-gambiza ƙarƙashin Ƙungiyar Jam'iyyun da suka damu kan abubuwan da ke faruwa wato Concerned Political Parties (CPP).
Sauran jam'iyyun da suke cikin wannan haɗaka sun haɗa da NNPP da ADC da APM da SDP da YPP da kuma ZLP.
Jam'iyyun hamayyar sun yi taron gamayyar ne karon farko a ranar Laraba inda aka yi wata ganawa tsakanin jagororin jam'iyyun bakwai a sakatariyar jam'iyyar SDP da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Sai dai gamin gambizar bai haɗa da Jam'iyyar Labour ba, wadda ɗan takararta ya zo na uku a babban zaɓen Najeriya na 2023.
LP ta bayyana cewa jam'iyyun da suka yi wannan taron ba su tuntuɓe ta ba.
Shugaban Jam'iyyar SDP, Shehu Musa Gabam, a jawabin da ya yi wa ƴan jarida bayan taron, ya ce matakin da suka ɗauka wani yunƙuri ne na rage ƙarfin ikon da jam'iyyar APC ke da shi a siyasar Najeriya.
Wannan yunƙuri na jam'iyyun adawa dai batu ne da al'ummar ƙasar da kuma ƴan siyasa ke ta tsokaci a kai.
Toh ko ya jam'iyya mai mulkin ta ji da wannan yunƙuri?
Ƙudirin gina wa mataimakin shugaban Najeriya sabon gida ya tayar da ƙura

Buƙatar gina wa mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, sabon gida na ci gaba da tayar da ƙura a kasar.
Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ne ya bukaci majalisar dattawan kasar ta amince da gina wa mataimakin shugaban kasar sabon gida wanda ake sa ran za a kashe kudi har naira biliyan 15.
Kungiyoyi masu rajin tabbatar da mulkin adalci da gaskiya na daga cikin wadanda suka yi kira ga majalisar dattawan ƙasar a kan ta ƙi amincewa da buƙatar ministan birnin tarayyar.
Wata wasiƙa da ƙungiyoyin suka aike wa shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio, ta yi kiran ya soke wannan buƙata a cikin kasafin ƙudin da ke gaban majalisar don kuwa ya saɓa wa tanadin mulkin adalci.
Auwal Musa Rafsan Jani shugaban kungiyar CISLAC, mai sanya ido a kan ayyukan majalisu da kuma yaki da rashawa a Najeriyar, ya shaida wa BBC cewa, wannan "wata dama ce ake nema ta wawure dukiyar kasa."
Kuna iya karanta cikakken labarin a nan:
Taron sauyin yanayi Najeriya ta je yi a Dubai ko sharholiya?

Asalin hoton, Getty Images
'Yan Najeriya na caccakar gwamnatin kasar a kan dumbin wakilan da ta aika zuwa taron sauyin yanayi na COP28 da ake gudanarwa a Dubai, a daidai lokacin da suke cikin matsin rayuwa.
Suna ikirarin cewa matakin wata manuniya ce ta rashin tausayi da rashin sanin ciwon kai daga gwamnati.
Wakilai kimanin 1,411 ne suke halartar taron daga Najeriya, daidai yawan mahalartan China, kasa ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya.
Al'ummar Najeriya na ganin wannan wata alama ce ta rashin tausayi daga ɓangaren gwamnati, kasancewar al'umma na fuskantar matsanancin yanayi a halin da ake ciki sanadiyyar tsadar rayuwa.
Ana ɗora laifin tsadar rayuwa da al'ummar ƙasar ke fuskanta kan manufofin gwamnatin Tinubu, ciki har da batun cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauye a harkar kuɗi.
Sai dai ministan yaɗa labaru na Najeriyar, Mohammed Idris ya ce ba dukkanin waɗanda suka tafi wurin taron daga Najeriya ba ne gwamnati ta ɗauki nauyin su.
Wata sanarwa da ya fitar ta nuna cewa mutum 422 ne cikin tawagar da gwamnatin tarayyar ta ɗauki nauyin tafiyar tasu.
Ga cikakken labarin a nan:










