Taron sauyin yanayi Najeriya ta je yi a Dubai ko sharholiya?

Asalin hoton, Getty Images
'Yan Najeriya na caccakar gwamnatin kasar a kan dumbin wakilan da ta aika zuwa taron sauyin yanayi na COP28 da ake gudanarwa a Dubai, a daidai lokacin da suke cikin matsin rayuwa.
Suna ikirarin cewa matakin wata manuniya ce ta rashin tausayi da rashin sanin ciwon kai daga gwamnati.
Wakilai kimanin 1,411 ne suke halartar taron daga Najeriya, daidai yawan mahalartan China, kasa ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya.
Al'ummar Najeriya na ganin wannan wata alama ce ta rashin tausayi daga ɓangaren gwamnati, kasancewar al'umma na fuskantar matsanancin yanayi a halin da ake ciki sanadiyyar tsadar rayuwa.
Ana ɗora laifin tsadar rayuwa da al'ummar ƙasar ke fuskanta kan manufofin gwamnatin Tinubu, ciki har da batun cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauye a harkar kuɗi.
Sai dai ministan yaɗa labaru na Najeriyar, Mohammed Idris ya ce ba dukkanin waɗanda suka tafi wurin taron daga Najeriya ba ne gwamnati ta ɗauki nauyin su.
Wata sanarwa da ya fitar ta nuna cewa mutum 422 ne cikin tawagar da gwamnatin tarayyar za ta ɗauki nauyin tafiyar tasu.
Shugaba Tinubu dai ya sha alwashin kyautata lamurra a Najeriya a matsayin sakayya ga wahalhalun da al'umma suka sha sanadiyyar ƙudurorinsa a ɓangaren tattalin arziƙi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Alƙaluma daga hukumar tarawa da rarraba kuɗaɗen haraji ta Najeriya (RMAFC), sun nuna cewa a lokacin irin wannan tafiya za a bai wa kowane minista ɗaya dala 900 kowace rana a matsayin kuɗin alawus na tafiya.
Mashawarta na musamman ga shugaban ƙasa kuma za a biya su dalar Amurka 800 a kowace rana, yayin da shugabannin hukumomi, da babban mai bincike na ƙasa, da manyan sakatarorin gwamnati, da babban akanta duk su ma akan biya su dalar Amurka 900 a kowace rana.
Idan aka haɗa lissafi za a ga cewa a lokacin wannan tafiya gwamnati za ta kashe dalar Amurka 11,700 a kan alawus ɗin tafiya na kowane minista ɗaya, sai kuma dalar Amurka 10,400 a matsayin kuɗin alawus ɗin tafiya na kowane mai bayar da shawara na musamman.
Idan aka musanya kuɗin zuwa naira, za a ga cewa kowane minista a lokacin wannan tafiya ta kwana 13 zai samu alawus na naira miliyan 10, wanda a tsarin albashi na Najeriya zai iya biyan albashin shekara biyar na ma'aikacin gwamnati da ke a mataki na takwas.
Martanin ƴan adawa
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, wanda ya bayyana tawagar Najeriya ta mutum 1,400 zuwa taron idan aka kwatanta da ta China a matsayin "abin takaici", ya nemi gwamnatin ƙasar ta "mayar da hankali kan rigegeniya da China wajen samar da kayayyaki" a madadin yawan wakilai.
Cikin wani jerin saƙo a dandalin X ranar Lahadi, Obi ya kwatanta kasafin kuɗin Najeriya da na China, da alƙaluman cigaban al'umma, da yawan jama'a, yana mai cewa Najeriya na "ƙarfafa bukukuwa da kuma nuna kai ne kawai".
"Akwai buƙatar mu dinga kashe kuɗi kan abin da ya zama dole da kuma wanda ƙasa take buƙata," a cewarsa.
Kazalika, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta nuna mamaki kan "ta yaya gwamnati za ta ɓatar da dukiyarta da kuma kashe kuɗaɗen ƙasar waje da ake buƙatarsu lokacin da 'yan ƙasa ke mutuwa saboda ƙarancin kayan abuƙata".
Ta kuma nemi gwamnatin ta APC ta bayyana sunayen wakilan Najeriya da kuma kuɗin da aka kashe a tafiyar.
Wakilan ƙasashen Afirka a taron COP28
Gwamnatin Kenya a gabashin Afirka ta haƙiƙance cewa mutum 51 kawai ta amince wa cikin 765 da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta lissafa a matsayin waɗanda suka halarci taron.
Tun da fari, 'yan Kenya sun bayyana rashin jin daɗinsu game da yawan wakilan ƙasar.
Gwamnatin ta ce bayan 51 da ta amince da su a hukumance, sauran wakilan sun fito ne daga ɓangaren 'yan kasuwa, da 'yan gwagwarmaya kan muhalli, da gwamnatoci yanki, da kuma majalisa, waɗanda ba ita ce ta ɗauki nauyin tafiyarsu ba.
Irin wannan martani ne ya biyo baya a Tanzania ma, inda 'yan ƙasar suka koka kan wakilai 763 da suka wakilci ƙasar a taron.
Ghana na da mutum 618 da suka wakilce ta, Afirka ta Kudu 410, sai kuma Zimbabwe mai 337.
Taro mafi yawan wakilai cikin shekara 30
Taron COp28 na wannan shekara da aka yi a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya kafa tarihin zama mai mafi yawan wakilai.
Sama da mutum 97,000 ne suka halarci taron da kansu - ba ta intanet ba.
Kusan ninki biyu ke nan na mutanen da suka halarci taron COP27 da aka yi a Sharm El-Sheikh na Masar shekarar da ta gabata.
Har zuwa lokacin COP28, taron na Masar ne ke riƙe da tutar mafi yawan wakilai tsawon shekara kusan 30 na tarukan.
Wannan shekara kuma an kafa tarihin yawan mutum 3,000 da suka halarci taron ta bidiyo kaɗai, wanda ya sa jimillar mahalarta taron na COP28 ta zama fiye da 100,000.
Hauhawar farashi ta kai kashi 27.3 cikin 100 a Najeriya a watan Oktoba, mafi girma tun watan Agustan 2005.
'Yan ƙasa na cewa gwamnati ba ta nuna wani ƙoƙari na rage kashe-kashen kuɗin da ba su zama dole ba.
Bugu da ƙari, gwamnatin Najeriya na tsananin buƙatar masu zuba jari daga ƙasashen waje domin haɓaka tattalin arzikin ƙasa na cikin gida.













