AFCON 2023: Yadda za a kece raini a zagayen kwata final

Asalin hoton, Getty Images
Bayan mako guda ana ɓarje gumi a wasannin zagaye na biyu inda tawagogin ƙasashe takwas suka samu ƙetarawa zuwa zagaye na gaba a gasar, yanzu an shirya kece raini a wasanni huɗu na matakin wasan daf da na kusa da karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2023.
An fafata a wasanni masu ban sha'awa tare da ban mamaki a zagaye na biyu, inda wasu daga cikin ƙasashen da ake sa ran cewa za su taka rawar gani kamar Senegal da Morocco suka kama hanyar gida.
Ga wasannin da za a kara a zagayen daf da na kusa da karshe da kuma ƙasashe da za su yi gwagwarmaya.
Najeriya da Angola

Asalin hoton, Getty Images
Super Eagles za ta kara da Angola a wasan farko na wannan zagayen a ranar Juma'a, 2 ga watan Fabrairu, a filin wasa na Félix Houphouët-Boigny da ke birnin Abidjan.
Wannan shi ne karon farko da ƙasashen biyu za su kara a gasar cin kofin nahiyar Afirka wanda Najeriya ta lashe sau uku a 1982 da 1994 da kuma 2013.
Ƙasashen biyu sun fafata a wasannin bakwai kafin gasar bana inda Najeriya ta lashe wasanni huɗu, ita kuma Angola ta na da nasara ɗaya, yayin da aka yi canjaras a wasanni biyu.
Nasarar ƙarshe da Angola ta samu a kan Najeriya ita ce wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya a watan Yunin 2004, inda aka tashi 1- 0.
Najeriya ta kasance ta 42 a jadawalin FIFA na yanzu, kuma a halin yanzu ita ce ta ɗaya a jerin ƙasashen da suka rage a gasar bayan an fitar da Morocco (13) da Senegal (20), da Tunisia (28), da Algeria (30) da kuma Masar (33). Yayin da Angola ita ce kurar baya (117) da ta rage a AFCON 2023.
Najeriya ta kai wannan matakin ne bayan ta doke Kamaru da ci 2- 0 a zagaye na biyu inda ita kuma Angola ta yi nasara kan Namibia da ci 3-0.
Idan har Angola za ta yi nasara dole sai ƴan wasan gabanta, Jacinto Dala da Gilberto da Mabululu su san yadda za a yi su sami galabar masu tsaron bayan Najeria, William Troost - Ekong da Calvin Bassey da Semi Ajayi a wannan karawar.
D.R Congo da Guinea

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
D.R Congo wadda da har yanzu ba ta yi nasara a gasar ba, za ta fafata da Guinea a wasan da za a buga ranar juma'a 2 ga watan Fabrairu a filin wasan Stade Olympique Alassane Ouattara da ke Abidjan.
Ƙasashen biyu sun fafata sau uku a matakin rukuni a gasar cin kofin nahiyar Afrika inda kowace ƙasa ta lashe wasa daya aka kuma yi canjaras ɗaya.
Karawarsu ta ƙarshe ta zo ne a a gasar 2004 a matakin rukuni, inda Guinea ta yi nasara da ci 2-1 sakamakon ƙwallayen da Titi Camara da Pascal Feindouno suka ci.
D.R Congo wadda ta ke harin kofin AFCON ɗinta na uku ta kai wannan matakin ne bayan ta doke Masar a bugun fenariti bayan wasan ta ƙare kunnen doki 1-1, yayin da ita kuma Guinea ta yi nasara kan Equatorial Guinea da ci 1-0.
Guinea za ta sami ƙwarin gwiwa sakamakon murmurewar fitaccen ɗan wasan gabanta, Serhou Guirassy, wanda ya yi fice a gasar Bundesliga ta bana amma duk da irin nasarorin da ya samu, wasanni biyu kacal ya buga a wasanni hudu na AFCON da aka buga kawo yanzu.
Mali da Cotê d’Ivoire

Asalin hoton, Getty Images
Cotê d’Ivoire mai masaukin baƙi ta taka rawar gani wajen kawar da mai riƙe da kofin gasar, Senegal a bugun fenareti a zagaye na biyu.
Hakan ya biyo bayan rashin ƙoƙarin da ta yi a wasanninta na rukuni inda ta yi rashin nasara a hannun Najeriya da Equatorial Guinea sannan aka zura ƙwallaye biyar a ragarta.
Za ta fafata da Mali a wasan da za su buga ranar asabar, 3 ga watan Fabrairu a filin wasan Stade de la Paix da ke Bouake.
Mali ta tsallake zuwa zagayen kwata fainal karo na bakwai a gasar cin kofin nahiyar Afirka bayan ta doke Burkina Faso da ci 2-1 a zagaye na biyu.
Ƙasashen biyu sun haɗu sau takwas a tarihin gasar inda Cote D’Ivoire ta yi nasara sau biyar saɓanin nasarar da Mali ta samu sau ɗaya yayin da aka yi canjaras a wasanni biyu.
Cotê d’Ivoire ta fuskanci ƙalubalen zura kwallo a raga a wannan gasar amma za ta sami ƙwarin gwiwa sakamakon dawowar ɗan wasan ganbanta Sébastien Haller, ganin cewa ƙwallo biyu kacal aka jefa a ragar Mali a gasar bana.
Cape Verde da Afrika ta kudu

Asalin hoton, Getty Images
Cape Verde wacce har yanzu ba a doke ta a gasar bana ba, za ta kara da Afirka ta Kudu a wasan da za fafata a ranr Asabar, 3 ga wata Fabrairu a filin wasan Charles Konan Banny da ke Yamoussoukro.
Afrika ta kudu wadd ta taɓa lashe gasar sau ɗaya a matsayin mai masukin baƙi a 1996, ta kai wannan matakin ne bayan ta doke Morocco da ci 2- 0, wanda kafin fara gasar ba a sa ran ta na ɗaya daga cikin ƙasashen da za su iya lashe gasar.
Ita kuma Cape Verde wadda wannan ne karon farko da take kaiwa wannan matakin, ta ƙetara ne bayan ta yi nasara a kan Mauritania da ci 1- 0.
Sau ɗaya ƙasashen biyu suka taɓa karawa a gasar cin kofin nahiyar Afrika inda wasan ya ƙare babu ci a gasar AFCON 2013.
Kocin Afrika ta kudu Hugo Broos zai dogara kan ‘yan wasansa Evidence Makgopa da Percy Tau da kuma Themba Zwane.
Cape Verde za ta sa ran cewa tsohon ɗan wasan Manchester United Bebe, mai shekara 33, zai taka rawar gani tare da Ryan Mendes mai shekara 34, da kuma dan wasan gefe na Sporting CP Jovane Cabral.










