Man Utd da Ronaldo an rabu, Arsenal na son Danilo, Guardiola ya kara lokaci

An wallafa

Hankalin Cristiano Ronaldo ya karkata tsakanin tafiya Newcastle United ko kuma kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya sakamakon raba gari tsakaninsa da Manchester United. 

Da wannan rabuwa Manchester United ta tsira da kusan fam miliyan 15.5 na albashin da za ta biya shi idan da ya ci gaba da zama a kungiyar har zuwa bazara.

Ita kuwa Chelsea na shirin fara tattaunawa ne a kan daukar Ronaldon bayan da daya daga cikin masu kungiyar Todd Boehly ke ganin damar daukar dan wasan a kyauta kodayake kociyanta Graham Potter na shakkun daukar dan wasan na Portugal.

Ana ganin Chelsea da Newcastle na nesanta kansu daga maganar daukar Ronaldon, yayin da ita Inter Miami ake ganin ta kawar da kanta daga kansa.

Kowacce daga cikin kwallayen da Ronaldo ya ci wa Manchester United a zuwansa na biyu ta raba ta da fam miliyan 1.2 

Arsenal na duba yuwuwar sayen dan wasan Palmeiras na gaba Danilo, na Brazil a watan Janairu.

A shirye Newcastle United take ta biya Borussia Monchengladbach fam miliyan 10 a watan Janairu a kan dan wasanta na gaba Marcus Thuram, na Faransa, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa. 

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya amince da karin shekara biyu a kwantiraginsa inda zai zauna har 2025. 

Dan wasan tsakiya na Faransa Aurelien Tchouameni, ya ce Liverpool ce ta fara zawarcinsa amma kuma Real Madrid yake son tafiya daga Monaco a bazaran nan idan dai har kungiyar ta Sifaniya ta neme shi.

Dan gaban Holland Memphis Depay, ya ce ba shi da tabbas kan makomarsa a Barcelona, kasancewar tsohuwar kungiyarsa Manchester United ta nuna sha’awar sayensa a lokacin bazara.

Wani mai bai wa Barcelona shawara ya mayar da kakkausan suka kan maganar da dan wasan da Manchester United ke zawarci Frenkie de Jong ya yi cewa kungiyar ta yi satar fitar da bayanan kwantiraginsa a bazarar da ta wuce.