Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool na son daukar Rice, Real Madrid ba ta neman Ronaldo
Liverpool za ta sa ido domin ganin rawar da dan wasan Ingila, kuma na tsakiyar West Ham Declan Rice, mai shekaru 23, zai taka a gasar cin Kofin Duniya da ake yi a kasar Qatar. (Football Insider)
Kociyan kungiyar Manchester City Pep Guardiola zai amince da sabon kwantiragi a kakar wasan 2025. (Sport - in Spanish)
Chelsea na gab da kammala yarjejeniya da Christopher Nkunku, wadda za ta ba da damar kawo mai kai hari na Faransa daga RB Leipzig ranar 1 ga watan Yulin badi. (Le10 Sport - in French)
Newcastle United na zawarcin dan wasan Juventus, mai kai hari na Sabiya Dusan Vlahovic, mai shekara 22, idan har suk samu damar zuwa Champions League a kaka mai zuwa. (Calciomercatoweb - in Italian)
Real Madrid ba ta wani shiri don sake dauko dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37 daga Manchester United a watan Junairu. (Marca - in Spanish)
Bournemouth ta shirya tsaf domin rantsar da shugaban riko Gary O'Neil a matsayin manajanta na dindindin, bayan tattaunawa da tsohon manajan Leeds United Marcelo Bielsa ta ki yin armashi. (Football Insider)
O'Neil na son aiki da tsohon manajan Blackpool Neil Critchley, a matsayin mataimaki idan ya samu aiki da Bournemouth job. (Sun)
Tsohon shugaban Real Madrid Zinedine Zidane ya amince ya maye gurbin Didier Deschamps a matsayin manajan Faransa bayan kammala gasar Kofin Duniya. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Tsohon manajan Burnley Sean Dyche, ya nuna sha'awar yin magana da Rangers, domin cike gurbin manajan kungiyar, bayan korar Giovanni van Bronckhorst. (Football Insider)
Ita kuwa Paris St-Germain ta wakilta wasu domin sa ido kan dan wasan gaba na Arsenal Gabriel Martinelli, mai shekara 21, domin ganin rawar da zai taka na wakiltar Brazil a gasar kofin duniya. (Todofichajes - in Spanish)
Tottenham na duba yiwuwar mai do da dan wasan tsakiya na Ukraine, Ruslan Malinovskyi. (Calciomercato - in Italian)