Busquet ba zai yanke shawarar gasar karshe da zai yi wa Sifaniya ba

An wallafa

Kyaftin din tawagar Sifaniya, Sergio Busquet ya ce ba zai yanke shawara ba kan ko wannan gasar da ake a Qatar ita ce ta karshe da zai yi.

Wannan ce Gasar Kofin Duniya ta hudu da dan wasan Barcelona zai buga, bayan lashe Kofin a 2010.

Mai shekara 34 ya dauki Kofin Gasar Nahiyar Turai a 2012 ''Ina mafarkin na kara daukar kofin duniya karo na biyu a Gasar Qatar.'' in ji Busquet.

''Ina murna da na halarci Gasar, ban damu da ita ce ta biyu ko ta hudu ba, ba zan yanke wani wa'adi ba.

Sifaniya za ta buga wasan farko a rukuni na biyar ranar Laraba da Costa Rica.

To sai dai kasar kan kasa cin wasan farko a rukuni a gasa uku baya da ta buga a wasannin da Fifa kan gudanar.

Wannan shi ne karon farko da Sifani da Costa Rica za su fafata a Gasar Cin Kofin Duniya.

Sai dai a karawa uku baya a wasannin sada zumunta, Sifaniya ce ta yi nasara a fafatawa biyu da canjaras daya.

Karon farko da za su fuskanci juna tun bayan 2011, an kuma ci kwallo 12 a wasannin da suka yi a tsakaninsu.