Arsenal na son Kerkez da Semenyo, Barca da Madrid na gogayya kan Fernandez

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na shirin taya ɗan bayan Bournemouth da Hungary Milos Kerkez, mai shekara 20, da ɗan gaba na gefe na ƙungiyar Antoine Semenyo, mai shekara 24, wanda ke taka wa tawagar Ghana leda. (CaughtOffside)
Kociyan Newcastle Eddie Howe, mai shekara 46, ba shi da niyyar barin ƙungiyar duk da cewa sunanshi na cikin waɗanda Ingila ke son zaɓa don cike gurbin kociyan ƙasar. (Telegraph)
Ɗan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 19, na dab da yarda da sabon kwantiragi da Manchester United. (Manchester Evening News)
Barcelona da Real Madrid kowacce na son sayen Alvaro Fernandez, na Sifaniya, mai shekara 21, ɗan bayan da Manchester United ta sayar wa Benfica a bazarar da ta gabata (Mirror)
Ana sa ran ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Denmark Christian Eriksen, mai shekara 32, ya koma ƙungiyarsa ta da Ajax idan kwantiraginsa ya ƙare a bazara mai zuwa. (Sun)
Tsohon ɗan bayan Liverpool da Kamaru Joel Matip, mai shekara 33, na duba yuwuwar yin ritaya daga wasan ƙwallon ƙafa. (Ruhr Nachrichten S04 a shafin X)
Kociyan Manchester City Pep Guardiola shi ne wanda hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta daɗe tana fatan bai wa aikin, hukumar da ba ta yi zaman ganawa da kowa ba sama da wata biyu bayan ta rufe karɓar takardun masu neman aikin. (Telegraph )
Everton tana son sayen ɗan wasan gaba na gefe na Stuttgart da Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo,Silas Mvumpa, mai shekara 26, a watan Janairu. (Football)
Tsohon kociyan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer, mai shekara 51, na tattaunawa da wata babbar ƙungiya da ba a ambata ba domin komawa kan sanarsa bayan da a baya ya yi watsi da ci gaba da tattaunawa domin zama kociyan Denmark. (Tipsbladet)
Liverpool ta zaɓi ɗan bayan Palmeiras Vitor Reis, mai shekara 18, a matayin wanda take ganin za ta saya nan gaba. Matashin ɗan wasan na Brzail, yana da sharaɗin duk ƙungiayr da za ta saye shi sai ta biya fam miliyan 84, kamar yadda yarjejeniyarsa ta tanada. (Football Insider)
River Plate na son tsawaita zaman aron da ɗan gaban Manchester City, Claudio Echeverri ke yi a ƙungiyar. A watan Janairu ne City ta sayi,matashin ɗan wasa, Echeverri, mai shekara 18, haifaffen Argentina, tare da sharaɗin cewa zai ci gaba da zama a River Plate, kafin ya tafi Ingila a watan Janairu na 2025. (TYC Sports)










