Chelsea ta dage kan Osimhen, Liverpool ta fara tunanin wanda zai maye gurbin Arnold

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta ci gaba da zawarcin Victor Osimhen, Liverpool na shirin rayuwa ba tare da Trent Alexander-Arnold ba, kuma Manchester United na tunanin sake siyan Alvaro Fernandez.
Galatasaray ba ta da shirin daukar dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen mai shekara 25 da ke zaman aro a kungiyar a matsayin dan was anta na din din din, yayin da ita kuma Chelsea ke ci gaba da zawarcinsa. (Teamtalk)
Daraktan Napoli Mauro Meluso ya tabbatar da cewa Osimhen yana da damar barin kungiyar kan farashi mai kyau a watan Janairu. (Metro)
Liverpool ta bayyana dan wasan Bayer Leverkusen dan kasar Holland Jeremie Frimpong, mai shekara 23, da Vanderson dan kasar Brazil dan da ke taka leda a Monaco mai shekaru 23 da kuma dan Italiya Michael Kayode mai shekaru 20 a matsayin wadanda take zawarcinsa idan har suka rasa Trent Alexander-Arnold. (Caught Offside)
Sai dai, akwai ci gaba da tattaunawar da kungiyar ke yi don tsawaita kwantiraginsu ɗan wasan na Ingila Alexander-Arnold, mai shekara 26. (Footbal Insider)
Dan wasan tsakiya na Italiya Jorginho, mai shekara 32, ya fi maida hankali kan makomarsa a Arsenal, duk da cewa ana alakanta shi da komawa Saudiyya. (Caught Offside)
An bayyana tsohon kocin Chelsea Thomas Tuchel a matsayin wanda ake ganin zai gaji Erik ten Hag lokacin da shugabannin kungiyar ta Manchester United za su yi wani zama a farkon makon nan. (Independent)
Manchester City za ta iya zawarcin dan wasan gaban Sporting Lisbon na Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, idan Barcelona ta iya zawarcin dan wasan gaban Norway Erling Haaland, mai shekara 24 daga Etihad Stadium. (Football 365)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Newcastle ce ke jagorantar fafatukar sayen dan wasan gaban Bournemouth na Ghana, Antoine Semenyo, mai shekara 24, a gasar Premier. (Teamtalk)
Liverpool na matukar bukatar amincewa da sabon kwantiragi da dan wasan bayan Netherlands Virgil van Dijk a yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan makomar dan wasan mai shekaru 33. (Footbal Insider)
Tsohon kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya yi watsi da tattaunawar karbar aikin Denmark saboda yana tattaunawa da wata babbar kungiya kan mukamin koci. (Tipsbladet)
Wolves na tunanin daukar kocin Aberdeen Jimmy Thelin, idan suka yanke shawarar korar Gary O'Neil. (Sun)
West Ham ta fara tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya da golan Ingila Fin Herrick mai shekaru 18. (Footbal Insider)
Torino na iya zawarcin dan wasan gaba na Napoli dan kasar Argentina Giovanni Simeone, mai shekara 29, sakamakon raunin da Duvan Zapata dan Colombia mai shekaru 33 ya yi a gwiwarsa. (Tuttosport)
Dan wasan tsakiya na Senegal Cheikhou Kouyate, mai shekara 34, yana daya daga cikin 'yan tsirarun 'yan wasan da Leeds United da ke tunanin saya. (Yorkshire Evening Post)










