INEC za ta baje-kolin sunaye da bayanan ‘yan takara a mazabu don tantance sahihancinsu

Shugaban hukumar zaben Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Daga ranar Juma’a 22 ga watan Yuli ne hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, za ta fara baje-kolin sunaye da bayanan ‘yan takarar mukamai daban-daban a mazabun kasar don tantance sahihancinsu.

 

INEC ta ce mutane za su iya zuwa mazabunsu don duba sunayen ‘yan takarar da ma bayanan da suka bayar, idan sun ga akasin hakan a bayanan da suka bayar to za su iya kai kara kotu.

 

Hajiya Zainab Aminu Abubakar, jami’ace a hukumar ta INEC, ta shaida wa BBC cewa idan jama’a ko sauran ‘yan takara sun ga akwai wani bayani da dan takara ya bayar wanda ba gaskiya ba ne to za su iya ka iwa kara.

 

Ta ce: "Kotu ce ke da damar gudanar da bincike kan bayanan da dan takarar ya bayar sannan ta kuma yanke hukuncin da ya kamata.”

 

Ta ce za a bar sunaye da bayanan ‘yan takarar a mazabu har zuwa wani lokaci saboda jama’a su samu damar zuwa su duba.

 

Jami’ar INEC ta kuma ce ya zuwa yanzu akwai kararraki 334 wanda aka shigar da su a kotu daban-daban da ke fadin Najeriya, kuma kararrakin sun shafi zabukan fid da gwani ne da jam’iyyu suka yi a watannin baya.

 

Hajiya Zainab Aminu Abubakar ta ce game da wadannan kararraki da aka shigar dama wadanda za a shigar a gaba kofar hukumar zaben a bude take a duk lokacin da aka nemi taje kotun a kan sharia’r to a shirye ta ke.

 

 Ta ce INEC ta sha alwashin ci gaba da taruka da zama na musamman da jam’iyyun siyasa domin ganin an kiyaye duk wasu dokoki na zaben da hukuma ta tsara da kuma tanade-tanaden da ta yi.

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta debarwa jam'iyyun suyasa wa'adin watanni biyu don gudanar da zaben fid da gwani domin warware duk wani rikici da ka iya biyo baya.