Zaɓen 2023: NNPP na son INEC ta tsawaita wa'adin zaɓukan fid da gwani

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Asalin hoton, OTHER

An wallafa

Wasu jam`iyyun siyasa sun jaddada cewa akwai bukatar hukumar zaɓen kasar ta duba yiwuwar kara musu wa'adin gudanar da zaɓukan fidda gwani, da mika sunayen 'yan takara na babban zaɓen da ke tafe.

Tuni dai hukumar zaben ta shata wa'adin uku ga watan Yuni mai zuwa domin jam'iyyun su mika mata sunayen 'yan takara, kuma kamar yadda ta shaida wa BBC a lokacin ta ce ba gudu ba ja da baya.

Jam'iyyar da ta nemi hakan a baya bayannan ita ce NNPP, kuma a cewar shugabanta Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali, suna bukatar isashen lokaci ne 'domin su kauce wa zaben tumun-dare' yayin tsayar da 'yan takarkarin.

Ya fada wa BBC cewa babu tantama INEC na tsoron kara lokaci ne don gudun kada jadawalin tsare-tsarenta ya lalace, to amma kuma idan jam'iyyun basu samu isashen lokacin tantance 'yan takara nagari ba, za su iya yin zaɓen tumun-dare.

''Su hangensu ba sa so a canza taimtebul wanda zai cunkusa musu ayyukansu yadda suka tsara su, har yazo ya shafi zaɓuka da za a yi a karshe.''

''To amma kuma shugabannin jam'iyyu muna ce musu fa in aka matsa ma jam'iyyu a cikin gaggawa aka ce dole a yi wannan abun, to ka gani in lokaci ya matso kowa ma in yazo sai ka mika masa ka ce ka je ka tsaya zaɓe.''

Shugaban sabuwar jam'iyyar ta NNPP mai alamar kayan marmari ya ce tun da farko sun nemi a kara musu wata biyu ne amma hukumar tace wata biyu ya yi yawa, daga nan suka nemi a basu wata ɗaya kuma suna fatan a wannan karon hukumar za ta saurari kokensu.

Zaben 2023
Bayanan hoto, Wasu daga cikin masu neman gaje kujerar shugaba Muhammadu Buhari da wa'adinda ke hanyar karewa

Ya kara da cewa a zaman karshe da suka yi Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya bukace su da su je su ci gaba da shirye-shiryensu tukuna, inda ya jaddada musu cewa tsawaita lokacin fidda gwanin ba mataki bane da zai yi gaban kansa ya dauka.

Sai dai abu ne mai wahala INEC ta iya tsawaita wa'adin, don a baya ta sanar da cewa itama tana da tarin ayyuka danƙare a gabanta, kuma ba za ta biya wa jam'iyyun bukatunsu ba ita kuma ta shiga matsala.

Ba jam'iyyar NNPP bace ta farko da ta nemi hukumar zaɓen ta tsawaita lokacin kammala zaben fidda gwanin daga 3 ga watan Yuni ba, sauran jam'iyyu kamar APC mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP sun bukaci hakan a baya amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.