ISIS ta sanar da kashe shugabanta tare da naɗa wani sabo

Yan ISI

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Kungiyar masu iƙirarin jihadi ta IS ta sanar da rasuwar shugabanta, Abu al-Hassan al-Hashemi al-Qurayshi.

Wani saƙon murya na kakakin ƙungiyar ya ce an kashe shi ne lokacin yana fada da wadanda ya kira "makiya ubangiji", amma kuma bai yi wani karin bayani ba.

A watan Maris ya zama shugaba bayan da tsohon shugaban ya kashe kansa a lokacin da dakarun Amurka suka kai masa hari a arewa maso yammacin Syria.

Kakakin ya ce sabon shugaban shi ne Abu al-Hussein al-Husseini al-Qurayshi amma ba a bayyana kasar da ya fito ba.

Sai dai ya bayyana Abu al-Hussein a matsayin gogaggen dan jihadi sa'annan ya bukaci 'yan kungiyar su yi masa mubaya'a.

A wani sako a shafin Telegram ƙungiyar al-Qaeda ta ce an dade da kashe shugaban na IS.

Ana tunanin cewa kungiyar IS na da mayaka tsakanin 6,000 zuwa 10,000 a kasashen Iraƙi da Syria.

Majalisar Ɗinkin duniya ta ce ƙungiyar na da mabiya sosai a ƙasashen Afghanistan da Somalia da kuma tafkin Chadi.