Isra'ila za ta yi bincike kan kisan yarinya Bafalasɗiniya Hind Rajab

Asalin hoton, Iyalin Hind Rajab
Rundunar sojin Isra'ila ta fara bincike kan wasu munanan hare-hare biyu da aka kai a Gaza sa'ilin yaƙin da aka tafka - waɗanda suka yi sanadin kashe wata yarinya Bafalasɗiniya ƴar shekara biyar mai suna Hind Rajab da kuma kisan ma'aikatan agaji 15.
Dukkanin hare-haren biyu sun yi matuƙar jan hankalin duniya.
Dakarun Isra'ila sun kashe Hind ce bayan ta shafe sa'o'i tana neman agajin masu aikin agaji na Falasɗinawa sa'ilin da take ɓuya a cikin wata mota bayan da aka kashe danginta waɗanda aka yi wa ruwan harsasai.
Sai dai rundunar sojin ba za ta yi bincike kan kisan da aka yi wa wasu ma'aikatan agaji bakwai masu aiki da ƙungiyar World Central Kitchen a watan Afurilun 2024 ba.







