'Yan Real Madrid da za su kara da Osasuna a La Liga

Vinicius and Benzema

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid za ta karbi bakuncin Osasuna a wasan mako na bakwai a gasar La Liga da za su fafata ranar Lahadi a Santiago Santiago Bernabeu.

Real Madrid tana matakin na biyu a kan teburin La Liga da maki 18 a wasa shida, bayan da Barcelona wadda ta yi karawa bakwai take ta daya mai maki 19.

Ita kuwa Osasuna mai maki 12 tana ta bakwai a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Wannan shi ne karon farko da Karim Benzema zai buga wa Real Madrid tamaula, bayan jinya da sha, sakamakon raunin da ya ji a Champions League.

Dan wasan tawagar Faransa ya ji rauni a wasan da Real ta je ta doke Celtic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni a babbar gasar Zakarun Turai ta bana cikin Satumba.

Wasan da suka buga a bara:

2021/2022

Spanish La Liga Laraba 20 ga watan Afirilun 2022               

  • Osasuna          1 - 3     Real Madrid   

Spanish La Liga Laraba 27 ga watan Oktoban 2021               

  • Real Madrid    0 - 0     Osasuna

Tuni Carlo Ancelotti ya sanar da 'yan wasan da za su buga masa karawar.

'Yan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin y Cañizares.

Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Camavinga, Valverde, Tchouameni da kuma D. Ceballos. 

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano. 

Wasannin da za a buga ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba a La Liga:

Espanyol da Valencia

Celta de Vigo da Real Betis    

Girona da Real Sociedad          

Wadanda suke kan gaba a cin kwallaye a La Liga:

  • Robert Lewandowski  Barcelona   9
  • Borja Iglesias   Real Betis        6
  • Iago Aspas       Celta de Vigo   5
  • Vinicius Junior Real Madrid           4
  • Alvaro Morata Atletico de Madrid      4
  • Rodrygo          Real Madrid            3
  • Federico Valverde       Real Madrid CF           3
  • Umar Sadiq     Real Sociedad 3
  • Alex Baena      Villarreal      3
  • Karim Benzema      Real Madrid CF           3
  • Alex Berenguer           Athletic Bilbao       3
  • Vedat Muriqi   Real Mallorca  3
  • Ezequiel Avila  Osasuna          3
  • Inaki Williams Athletic de Bilbao       3
  • Joselu  Espanyol  3
  • Brais Mendez  Real Sociedad 3