Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Real Madrid da za su kara da Osasuna a La Liga
Real Madrid za ta karbi bakuncin Osasuna a wasan mako na bakwai a gasar La Liga da za su fafata ranar Lahadi a Santiago Santiago Bernabeu.
Real Madrid tana matakin na biyu a kan teburin La Liga da maki 18 a wasa shida, bayan da Barcelona wadda ta yi karawa bakwai take ta daya mai maki 19.
Ita kuwa Osasuna mai maki 12 tana ta bakwai a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Wannan shi ne karon farko da Karim Benzema zai buga wa Real Madrid tamaula, bayan jinya da sha, sakamakon raunin da ya ji a Champions League.
Dan wasan tawagar Faransa ya ji rauni a wasan da Real ta je ta doke Celtic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni a babbar gasar Zakarun Turai ta bana cikin Satumba.
Wasan da suka buga a bara:
2021/2022
Spanish La Liga Laraba 20 ga watan Afirilun 2022
- Osasuna 1 - 3 Real Madrid
Spanish La Liga Laraba 27 ga watan Oktoban 2021
- Real Madrid 0 - 0 Osasuna
Tuni Carlo Ancelotti ya sanar da 'yan wasan da za su buga masa karawar.
'Yan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin y Cañizares.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Camavinga, Valverde, Tchouameni da kuma D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.
Wasannin da za a buga ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba a La Liga:
Espanyol da Valencia
Celta de Vigo da Real Betis
Girona da Real Sociedad
Wadanda suke kan gaba a cin kwallaye a La Liga:
- Robert Lewandowski Barcelona 9
- Borja Iglesias Real Betis 6
- Iago Aspas Celta de Vigo 5
- Vinicius Junior Real Madrid 4
- Alvaro Morata Atletico de Madrid 4
- Rodrygo Real Madrid 3
- Federico Valverde Real Madrid CF 3
- Umar Sadiq Real Sociedad 3
- Alex Baena Villarreal 3
- Karim Benzema Real Madrid CF 3
- Alex Berenguer Athletic Bilbao 3
- Vedat Muriqi Real Mallorca 3
- Ezequiel Avila Osasuna 3
- Inaki Williams Athletic de Bilbao 3
- Joselu Espanyol 3
- Brais Mendez Real Sociedad 3