Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool da Newcastle na zawarcin Mbeumo
Liverpool da Newcastle na son dan wasan baya na Kamaru mai taka leda Brentford Bryan Mbeumo mai shekara 25. (Sun)
Manchester City na sahun gaba a masu son dan wasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz, inda su ma kungiyoyin Real Madrid da Liverpool na cikin masu zawarcin dan wasan na Jamus. (Caught Offside)
Dan wasan baya na Santos, Joao Victor de Souza, 18, na daga cikin wadanda kungiyar Chelsea ke so, sai dai da alama ita ma kungiyar Barcelona na zawarcin dan wasan dan asalin ƙasar Brazil. (AS - in Spanish)
Mai tsaron gida na Ivory Coast mai taka leda a Sporting Ousmane Diomande, mai shekara 20, na tattaunawa da kocin Manchester United Ruben Amorim domin sake hadewa da shi a Old Trafford. (Metro)
Jorge Mendes na kokarin ganin an cimma matsaya kan dan wasan Portugal mai taka leda a Sporting Geovany Quenda, wanda Manchester United ma ke zawarcinsa. (Teamtalk)
Dan wasan tsakiya na Norway, mai taka leda a Rosenborg Sverre Nypan, mai shekara 17, ba zai koma Manchester United ba har sai an bashi tabbacin kan rawar da zai taka a kungiyar. (Give Me Sport)
Tsohon manajan riko na Manchester United Ruud van Nistelrooy, na son zama a kungiyar ta gasar Premier, a daidai lokacin da ake tsaka da hasasshen kungiyoyin Southampton da Wolves da kuma Crystal Palace na son daukar shi. (Football Insider)
West Ham ta shirya domin sayar da dan wasa Guido Rodriguez, mai shekara 30, a watan Junairu, inda ake sa ran zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Real Betis. (Estadio Deportivo - in Spanish)
Liverpool ka iya sanya fam miliyan 17 kan dan wasan tsakiya na Faransa Rayan Cherki, mai shekara 21, inda ita kuma kungiyar Lyon tagabatar da tayin fam miliyan 29. (TBR)