Ruben Amorim ya amince ya horas da Manchester United, Arsenal na neman Bryan Mbeumo

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mai horas da ƙungiyar Sporting, Ruben Amorim ya amince ya zama kocin Manchester United, bayan ƙungiyar ta kori Erik ten Hag a ranar Litinin. (Manchester Evening News)

Shi ma tsohon kocin Borussia Dortmund, Edin Terzic ya na kan gaba a jerin masu horas da ƙwallo da Manchester United ke zawarci bayan an naɗaThomas Tuchel a matsayin kocin Ingila. (Sun)

Arsenal ta ƙara ƙaimi a zawarcin ɗan wasan gaban Brentford da Kamaru mai shekara 25, Bryan Mbeumo. (Football Insider)

Liverpool na shirin gabatar da tayin ɗan wasan Nottingham Forest kuma ɗan Brazil mai shekara 22, amma alamu na nuna cewa za ta yi takara da Chelsea idan har tana son ɗaukar ɗan wasan bayan. (Teamtalk)

Kocin Brentford, Thomas Frank na cikin waɗanda Manchester United ke fatan su maye gurbin Ten Hag. (ESPN)

Manchester United ta tsara masu horas da ƴan wasa aƙalla Biyar da ta ke fatan za su gaji Ten Hag. (Sky Sports)

Watakil ɗan wasan gaban Sweden, Alexander Isak mai shekara 25, zai raba gari da Newcastle a kakar wasan baɗi. (Football Insider)

Liverpool da Benfica da kuma Turkiyya na bibiyar ɗan wasan tsakkiya midfielder Orkun Kokcu, 23. (Record - in Portuguese), external

Arsenal ta ƙi amincewa da tayin ɗan wasan ta ɗan asalin Brazil (ESPN), external

Manchester United na sha'awar ɗan wasan Sporting mai shekara 17 kuma ɗan Portugal, Geovany Quenda. (A Bola - in Portuguese)