Farashin mai ya sauka bayan cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran
Farashin hannayen jari ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Asiya, yayin da farashin mai ya ragu, bayan sanar da cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran.
Farashin ɗanyen man fetur na Brent ya fara sauka da kusan kashi huɗu cikin ɗari, inda ya ragu zuwa ƙasa da dala 84 kan kowace ganga.
Farashin man ya sakko ƙasa duk da rashin ƙarin bayani kan abun da ke ƙunshe cikin yarjejeniyar, abun da ke nuna yadda 'yan kasuwa suka yi imanin cewa komi zai daidaita da zarar an sake buɗe mashigar Hormuz.
Kafin rikicin, kusan kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas na duniya na bi ta wannan muhimmiyar hanya da ke yankin Tekun Fasha.
A lokacin da faɗan ya ɓarke, Iran ta kusan hana zirga-zirgar jiragen ruwa ta wannan mashiga gaba ɗaya.