Vinicius zai bar Madrid, United da Chelsea na rububin neman Dorgu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid na fakon Trent Alexander-Arnold, Newcastle na son Bryan Mbeumo, Arsenal na zawarcin Mohammed Kudus, da sauran su.

Dan wasan bayan Liverpool na Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26 ne dan wasan da Real Madrid ta fi so ta karfafa bayanta da shi. (AS - Spanish)

Newcastle United ta sanya dan wasan Kamaru Bryan Mbeumo a cikin jerin sunayen yan wasan da take nema, inda Brentford ta sanya farashinsa a kan kusan fan miliyan 50 (Football Isider)

Arsenal na zawarcin dan wasan West Ham na Ghana Mohammed Kudus, mai shekara 24, don maye gurbin dan wasan gaban Belgium Leandro Trossard mai shekaru 29, wanda kungiyar Al-Ittihad ta Saudi Pro League ke zawarcinsa. (Mirror)

Dan wasan gaban Reims dan kasar Ivory Coast, Oumar Diakite, mai shekara 20 ne zai kasance dan wasan da Crystal Palace za ta fi mayar da hankali kansa. (Sun)

Manchester United da Chelsea sun bi sahun Tottenham wajen neman dan wasan bayan Denmark Patrick Dorgu, mai shekara 20, daga Lecce. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Ingila Lewis O'Brien, mai shekara 26, da alama yana shirin komawa Los Angeles FC a kan fam miliyan 7. (Sun)

Barcelona na bibiyar halin da Rafael Leao ke ciki a AC Milan idan dan wasan na Portugal, mai shekara 25, ya samu. (Mundo Deportivo)

Real Madrid ta fara nuna shakku kan kwazon Vinicius Jr a kungiyar kuma suna fargabar zai yi tunanin barin kungiyar, inda Al-Hilal ke sha'awar daukar dan wasan gaban Brazil mai shekara 24. (Sport Spanish)

Chelsea da Paris St-Germain ma suna zawarcin Vinicius Jr kuma jami'an Real Madrid za su gana da wakilansa nan da 'yan makonni domin tattauna makomarsa. (Marca Espanya)

Santos na tattaunawa kan dawo da Neymar kungiyar a lokacin da kwantiraginsa da Al-Hilal zai kare a bazara mai zuwa (AS -Spanish)

Lazio tana daya daga cikin kungiyoyin da ke son siyan James Rodriguez idan dan wasan na Colombia, mai shekara 33, ya kawo karshen zamansa da Rayo Vallecano. (Mundo Deportivo Spanish)