Man Utd da Real Madrid na son Sanchez, Tottenham ta ƙi yarda a raba ta da Romero

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na sa ido a kan ɗan bayan Sevilla Juanlu Sanchez mai shekara 21. (AS - in Spanish)

Ita Real Madrid na son Sanchez. (Teamtalk)

Ɗan wasan gaba na gefe Antony, na Brazil ba ya son barin Manchester United duk da sha'awarsa da Fenerbahce ke yi. (ESPN)

Ƙungiyoyin babbar gasar Turkiyya ta Super Lig da suka haɗa da Istanbul Basaksehir da Fenerbahce da Besiktas da kuma Eyupspor sun haƙura da neman Kieran Trippier bayan da Newcastle ta fito ƙarara ta ce tana son ci gaba da zama da tsohon ɗan bayan na Ingila mai shekara 33. (Sky Sports)

Aston Villa ta ɗauki Jhon Duran da matsayi sosai bayan da ta yi watsi da tayi 40 a kan matashin ɗan wasan na Colombia mai shekara 20 a lokacin bazara. (Mirror)

Kociyan Newcastle Eddie Howe da darektan wasanni na ƙungiyar Paul Mitchell sun ɗinki ɓarakar da ke tsakaninsu inda a yanzu suka mayar da hankali kan ƴan wasan da za su saya a watan Janairu, da suka haɗa da ɗan bayan Crystal Palace Marc Guehi, na Ingila mai shekara 24. (Telegraph)

Chelsea ta tattauna kan barin filinta na Stamford Bridge, domin ta gina wani sabon filin wasan a Earl's Court. (Guardian)

Ɗan bayan Scotland Liam Cooper, na dab da komawa CSKA Sofia, bayan da kwantiraginsa ya ƙare ya bar Leeds a ƙarshen kakar da ta wuce. (Football Insider)

Ɗan kasuwar Amurka John Textor na da ƙwarin gwiwar cewa zai kammala sayen Everton cikin mako huɗu. (Guardian)

An hana Andy Mangan na Stockport County shiga cikin masu horad da Real Madrid bayan da aka hana shi takardar izinin aiki saboda yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga Turai. (Times )

Tottenham ta yi watsi da buƙatar Manchester United da Real Madrid da Paris St-Germain ta neman ta sayar musu da ɗan bayanta na Argentina Cristian Romero. mai shekara 26 a lokacin kasuwar 'yan wasa (TyC Sports, daga Mail)

Galatasaray na sha'awar aron matashin ɗan wasan gaba na gefe na Chelsea Carney Chukwuemeka na Ingila. (Teamtalk)