Arsenal za ta kara da Tottenham da Atalanta da Man City cikin Satumba

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal za ta buga wasa biyar cikin Satumba da ya haɗa da uku a Premier League da Champions League da kuma League Cup.

Tottenham za ta karɓi bakuncin Arsenal a wasan hamayya karawar mako na huɗu a Premier League ranar 15 ga watan Satumba.

Wasa tsakanin Tottenham da Arsenal a 2023/2024

Premier League ranar Lahadi 28 ga watan Afirilun 2024

  • Tottenham 2 - 3 Arsenal

Premier League ranar Lahadi 24 ga watan Satumba 2023

  • Arsenal 2 - 2 Tottenham

Haka kuma Gunners za ta je Italiya domin karawa da Atalanta a wasan farko a cikin rukuni a Champions League ranar Alhamis 19 ga watan Satumba.

Wannan shi ne karon farko da Atalanta da Gunners za su kece raini a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai a tsakaninsu.

Wasa na uku da Arsenal za ta yi a waje a jere a Satumba, shi ne a gidan Manchester City a mako na biyar a Premier League ranar 22 ga watan Satumba.

Wasa tsakanin Manchester City da Arsenal a 2023/2024

Premier League ranar Lahadi 31 ga watan Maris 2024

  • Man City 0 - 0 Arsenal

Premier League ranar Lahadi 8 ga watan Oktoba 2023

  • Arsenal 1 - 0 Man City

Community Shield ranar Lahadi 6 ga watan Agusta 2023

  • Arsenal 1 - 1 Man City

Daga nan ne Gunners za ta karɓi bakuncin Bolton a League Cup da za su kece raini a Emirates ranar 25 ga watan Satumba.

Wasa na karshe da Arsenal za ta yi a cikin watan Satumba, shi ne wanda Leicester City za ta je Emirates a mako na shida a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar 28 ga watan Satumba.

Wasa tsakanin Arsenal da Leicester City a 2021/2022

Premier League ranar Lahadi 13 ga watan Maris 2022

  • Arsenal 2 - 0 Leicester

Premier League Asabar 30 ga watan Oktoba 2021

  • Leicester 0 - 2 Arsenal

Arsenal tana mataki na uku a teburin Premier League da maki bakwai, bayan da ta ci wasa biyu da canjaras ɗaya.

Wasannin da Arsenal za ta kara cikin Satumbar

Premier League ranar Lahadi 15 ga watan Satumba

  • Tottenham da Arsenal

Champions League ranar Alhamis 19 ga watan Satumba

  • Atalanta da Arsenal

Premier League ranar Lahadi 22 ga watan Satumba

  • Man City da Arsenal

League Cup ranar Laraba 25 ga watan Satumba

  • Arsenal da Bolton

Premier League ranar Asabar 28 ga watan Satumba

  • Arsenal da Leicester