Yamal ne gwarzon La Liga na Agusta da koci Flick na Barca

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal ya lashe ƙyautar gwarzon matashin La Liga na watan Agusta, bayan da ya ci ƙwallo ya kuma bayar da huɗu aka zura a raga.

Haka kuma koci, Hansi Flick na Barcelona shi ne fitatce a watan na Agusta, bayan da ƙungiyar ta lashe wasa huɗu a jere da fara kakar bana.

Mahukuntan La Liga kan karrama ɗan wasa da kocin da suka fi yin bajinta a duk wata a gasar a zaben da ake tsakanin magoya baya a intanet.

A wasan makon farko da Barcelona ta je ta ci Valencia 2-1, Yamal ne ya bai wa Robert Lewandowski, ƙwallon da aka fara cin Barcelona daga baya ta lashe karawar.

A mako na biyu da Athletic Club a Estadi Olimpic, Yamal mai shekara 17 ne ya fara cin ƙwallo a fafatawar da Barcelona ta yi nasara 2-1.

Yamal, wanda ya lashe Euro 2024 a Jamus daga nan ya bayar da ƙwallo uku aka zura a rawa a wasan da Barcelona ta doke Rayo 2-1 da wanda ta caskara Valladolid 7-0.

Matashin ɗan wasan na taka rawar gani a La Liga da Barcelona a bana, wanda ya buga mata dukkan karawa huɗu da fara kakar nan.

Haka kuma kociyan Barcelona, Hansi Flick shi ne gwarzon mai horar da tamaula a La Liga a watan Agusta, bayan da ƙungiyar ta lashe dukkan karawa huɗu da cin ƙwallo 13, inda uku suka shiga ragarta.