Real Madrid ta caskara Celtic ta ja ragamar rukuni na shida

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta caskara Celtic da ci 5-1 a wasan karshe a cikin rukuni na shida a Champions League ranar Laraba a Santiago Bernabeu.
Minti na shida da take leda Real ta fara zura kwallo ta hannun Luka Modric a bugun fenariti.
Kungiyar Sifaniya ta kara na biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga ta hannun Rodrygo a minti na 21.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Real ta kara kwallo hudu ta hannun Marco Asensio da Vinicius Junior da kuma Federico Valverde.
Sauran minti shida a tashi daga wasan Celtic ta zare daya ta hannun Jota.
A dayan wasan RB Leipzig ce ta je ta doke Shakhtar 4-0.
Real Madrid ta casa Celtic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni ranar 6 ga watan Satumba a Scotland.
Da wannan sakamakon Real Madrid ta hada maki 13 a karawa shida a rukuni na shida, sai RB Leipzig mai 12 da Shakhtar Donetsk mai shida da Celtic mai maki biyu.
Real Madrid ce ke rike da Champions League da ta dauka a bara, kuma na 14 jumulla.
Ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba za a raba jadawalin zagaye na biyu na kungiyoyi 16 da za su ci gaba da buga gasar ta Zakarun Turai.
Wasan da Real da Celtic suka fafata a tsakaninsu.
2022/2023
Champions League Laraba 2 ga watan Nuwamba
- Real Madrid. 5 - 1 Celtic
Champions League Talata 6 ga watan Satumba
- Celtic 0 - 3 Real Madrid
1979/1980
European Cup Laraba 19 ga watan Maris 1980
- Real Madrid 3 - 0 Celtic
European Cup Laraba 5 ga watan Maris 1980
- Celtic 2 - 0 Real Madrid
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis López.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger da F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde da D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da Mariano.










